Connect with us

Uncategorized

Kimanin shugabannan Fulani 66 da wasu ‘yan Arewa 1000 sun janye daga PDP zuwa APC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar APC sun marabci kimamin shugabanan Fulani 66 da wasu ‘yan Arewa da yawar 1000.

Jam’iyyar PDP ta rasa wadannan yawar mambobin ne daga Jihar Sokoto a yayin da shugabannan suka kudura da janye daga jam’iyyar PDP zuwa APC da akan cewa basu samu kulawa ta kwarai ba a jam’iyyar PDP.

Naija News Hausa ta gane da cewa mutanen da ke daga kananan hukumomin Jihar Sokoto kammar; Silame, Wamakko, Tangaza, Gudu, Yabo, Shagari, Binji da karamar hukumar Tureta sun yi murabus ne da PDP suka kuma komawa jam’iyyar APC da fadin cewa shugabannan jam’iyyar PDP basu basu kulawa ta musanman ba, sa’anan sun bukaci kayakin noma don gudanar da ayukan su a gonakin su.

Alhaji Shehu Aliyu, ciyaman na kungiyar Fulani na tarayyar kasar Najeriya, ya bayyana da cewa mutanen na a shirye don bada goyon baya ga jam’iyyar APC ga zaben gwamnoni da kuma ta gidan majalisar jihar.

Ko da shike, Ciyaman na kungiyar manyan jam’iyyar APC na Jiahr, Alhaji Aminu Tambari Tafida, ya gabatar da cewa jam’iyyar APC zasu bada isashen kulawa da tallafi ga Fulanin Jihar. Musanman wajen samar masu da kayakin noma da kayakin alfahari da zai taimaka masu ga rayuwa.