Connect with us

Uncategorized

2019: INEC ta gabatar da lokacin da za a fara zaben Gwamnoni a ranar Asabar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar  gudanar da zaben kasa, INEC ta bayyana lokacin da za a fara hidimar zaben gwamnonin Jiha da ‘yan Gidan Majalisar Jiha da za a soma yi ranar Asabar 9 ga watan Maris a Jihohin kasar Najeriya.

Naija News ta gane da sanarwan ne kamar yadda shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar a wata ganawa da suka yi ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja, da cewa kowace runfar zabe zata fara hidimar ne a misalin karfe takwas (8am) na safiyar ranar Asabar ta gobe.

Farfesa Mahmood ya kara da cewa an riga an samar da kayaki ga kowace jiha harma da birnin tarayya hade da kananan hukumomi a ranar Jumma, 8 ga watan Maris, 2019.

“Kamin gobe Asabar, ina da tabbacin cewa dukan kayakin zabe da mallaman zabe sun halarci runfunar zabe. Da wannan shiri kuma, muna da bugun gaba da cewa hidimar zabe zai fara a kowace runfar zabe a daidai karfe 8 na safiya” inji Farfesa Yakubu.

Naija News na da sani cewa wannan hidimar zaben gwamnoni zai kasance ne a jihohi 29 a kasar, a yayin da za a kuma yi zaben ‘yan gidan majalisar jiha 991 a jihohin hade da Ciyamomi 6 da Kansiloli 62 a birnin Abuja.