Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 8 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 8 ga Watan Maris, 2019

 

1. Kotu na barazanar kame Bukola Saraki, shugaban Sanatocin Najeriya

Kotun Koli ta birnin tarayya, ta kafa baki ga barazanar kame sanata Bukola Saraki da Sakataren gidan Majalissar dokoki, Mohammed Sani-Omolori akan wata mataki da ya kamata sun dauka tun ranar 13 ga watan Yuni ta shekaran 2018 da ya gabata.

Naija News ta gane da cewa kotun ta bukaci sanata Saraki da Sani-Omolori da rantsar da Ofisan sojojin sama, Isaac Mohammed Alfa (rtd) a matsayin sanata da zai wakilci Gabashin jihar Kogi.

2. Biafra: Nnamdi Kanu ya gabatar da zancen Biafra ga hukumomin kasar Turai

Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya dauki zancen kafa yankin Biafra a kasar Najeriya zuwa hukumomin kasan Turai a Brussels, ta kasar Belgium.

Naija News Hausa ta gane da cewa Nnmadi Kanu da mataimakin sa, Uche Mefor sun gana don tattaunawa da hukumomin kasan Turai a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019.

3. Ban mutu ba, Ina Lafiya Kalau – Masoyin Buhari da ya sha ruwar kwata

Jita-jita mutuwar Aliyu ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo duka, amma abin mamaki Aliyu Mohammed Sani ya fito da bayyana da cewa bai mutu ba. kamar yadda gidan jaridan Daily Trust ke bada tabbacin haka.

“Alkawari ne nayi da cewa idan har shugaba Muhammadu Buhari ya lashe tseren takaran kujerar shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga zaben 2019, zan yi wanka da ruwar kwata, zan kuma sha kwata”

4. Karanta ka ga irin mutanen da INEC ba zata ba wa takardan komawa ga mulki ba

Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta gabatar da cewa ba zata bada takardan komawa ga mulki ba ga duk wani dan takara da ya lashe zabe amma ta hanyar tanzoma kowa karya dokar zaben kasa a zaben ranar Asabar.

Wannan itace daya daga cikin bayanin da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar a wajen zaman tattaunawa da hukumar ta yi a ranar Alhamis da ta gabata akan tsaro lokacin zabe da wata rukuni a nan birni Abuja.

5. Shugaba Buhari da matarsa Aisha sun isa Daura don zaben ranar Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis da ta gabata da matarsa sun isa garin Daura a yayin da suke jirar ranar Asabar ya iso don su jefa kuri’ar su ga zaben gwamnoni da ta gidan majalisar wakilan jiha.

Naija News ta gane da shigar shugaba Buhari ne a yayin da ya sauka daga jirgin sama a misalin karfe 6:50 na maraicen ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019.

6. Jam’iyyar PDP na da amsa da zasu bayar ga zargin da ke kansu – inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa Jam’iyyar adawa, PDP na da amsoshi da zasu bayar akan zargin kashe-kashen tattalin arzikin kasa da suka yi watsi da ita tun daga shekarar 1999 har zuwa shekarar 2014 a kasar.

Shugaban ya bayyana zargin ne a lokacin da yake wata ganawa a ranar Alhamis da ta gabata tare da shugabannan hukumar ma’aikatan kasa a nan birnin Abuja.

7. Hukumar INEC sun gabatar da lokacin da za a fara zaben ranar Asabar a jihohin kasar

Naija News ta gane da sanarwan ne kamar yadda shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar a wata ganawa da suka yi ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja, da cewa kowace runfar zabe zata fara hidimar ne a misalin karfe takwas (8am) na safiyar ranar Asabar ta gobe.

Farfesa Mahmood ya kara da cewa an riga an samar da kayaki ga kowace jiha harma da birnin tarayya hade da kananan hukumomi a ranar Jumma, 8 ga watan Maris, 2019.

8. Atiku yayi gabatarwa ga ‘yan Najeriya akan zaben Gwamnoni da Majalisar wakilan Jiha

Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga al’ummar Najeriya duka da fitowa ranar Asabar don jefa kuri’ar su ga dan takaran su ga zaben gwamnoni.

Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar da wannan sanarwan ne ga ‘yan Najeriya a ranar Alhamis a yanar gizo cikin wata bidiyo da aka tsarafa. Ya bukaci ‘yan Najeriya da fita ranar Asabar don jefa kuri’ar su a matsayin ‘yan kasa.

9. Gwamna Wike na zargin Amaechi da kame mambobin jam’iyyar PDP

Gwanan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya zargi Ministan Tafiye-tafiye, Mista Chibuike Rotimi Amaechi da Rundunar Sojojin Najeriya na kadamar da kame mambobin jam’iyyar PDP a Jihar Rivers.

Wike da zargin cewa Amaechi da rundunar sojojin na hakan ne don tayar da farmaki da kuma bada dama ga hukumar INEC don dakatar da zaben Jihar.

Karanta cikkakun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa