Connect with us

Labaran siyasa

Wasu ‘Yan Ta’adda sun haska wuta ga wata makaranta a Jihar Ebonyi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Da safiyar yau Asabar, wasu ‘yan ta’addan sun hari mallaman gudanar da hidimar zabe a Jihar Ebonyi.

Abin ya faru ne misalin karfe biyu (2am) na safiyar yau 9 ga watan Maris, 2019 a yayin da ake jiran ‘yan awowi kadan da fara zaben gwamnoni da ta gidan majalisar jihohin kasar Najeriya. Wasu ‘yan ta’addan da ba a gane da su ba,  sun hari malaman aikin zabe na Jihar da farmaki har sun kone makarantar sakandari da ke a yankin, inda ake gudanar da hidimar zabe a kowace lokaci.

Mazuanin unguwar sun bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan ta’addan sun fada wa wajen ne misalin asuba’i suka kuma haska wuta ga makarantar sakandari da ke a Okposi Umuoghara (07), a nan karamar hukumar Ezza ta Jihar.

Ko da shike a lokacin da aka karbi wannan rahoto, an kira kwamishanan ‘yan sandan jihar, Farfesa Godswill Obioma, amma bai bada wata bayani ba a lokacin.

Idan akwai wata bayani da ta biyo a baya, Naija News Hausa za ta gabatar da hakan.

Ka samu karin bayanai a shafin Siyasa a layin mu na LABARAN SIYASA