Siyasa: Atiku Abubakar ya saki sunan ‘yan cin hancin da rashawa 30 da ke aiki da Buhari

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa sunayen masu cin hanci da rashawa da shugaba Buhari ke shugabanci da su.

Ko da shike ‘yan Najeriya da daman su zuba wa Atiku kalaman bacin rai da zage-zage don rashin tsayawar shi ga wajen muhawarar dan takaran shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta wuce kamar yadda Naija News ta bayar da safen nan. Dan takaran ya zo da baya ga shafin nishadin twitter din sa ya roki ‘yan Najeriya da suyi masa gafara da wannan. kuma ya iya bayyana dalilin da ya sa bai iya tsayawa ba ga wannan zaman.

Duk da haka Atiku Abubakar a ranar jiya, Lahadi 20 ga watan Janairu, 2019 ya wallafa sunayen mutanen da suke da liki da halin cin hanci da rashawa da kuma ke aiki tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Mun sami sani da cewa, Phrank Shaibu daya daga cikin masu yada sanarwa ga Atiku ne ya saki sunayen. ya bayyana da cewa ko da shike da yawa cikin su ‘yan Jam’iyyar PDP ne, sauran kuwa sun gudu ne zuwa nashi Jam’iyyar don neman tsira da ga hukumar hukumta cin hanci da rashawa.

Sunayen na kamar haka:

Bola Tinubu, Abba Kyari, Adams Oshiomhole, Abdullahi Adamu, Babachir Lawal, Folarin Coker, Lai Mohammed, Tukur Buratai, Hadi Sirika, Aisha Buhari, Adedayo Thomas, Adamu Muazu, Iyiola Omisore, Abdulrasheed Maina, Musiliu Obanikoro, Orji Uzor Kalu, Isa Yuguda of Bauchi, Godswill Akpabio, Yemi Osinbajo, Abdullahi Umar Ganduje, Ahaji Seminu Turaki, Alhaji Junaid Abdullahi, Alhaji Aliyu Wammako, Hope Uzodinma, Rotimi Amaechi, Alhaji Abdul’aziz Yari, Maikanti Baru, Ayodele Oke.

 

Karanta kuma: Dr. Amina Abubakar Bello Sani Bello ta ba wa Mata 150 tallafin kudi na 10,000 ga kowanansu a Mariga yankin  Jihar Neja

Kalla: Shugaba Muhammadu Buhari a garin Maiduguri

https://www.youtube.com/watch?v=aqWjkfWvrOk