Connect with us

Uncategorized

Gobarar wuta ya kone Gidaje 60 a Jihar Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin gidaje 60 suka kone kurmus sakamakon kamun wutar. Dabbobi da kayakin rayuwar al’umma duk ta kame da gobarar wutar.
Abin ya faru ne a kauyan Barebari da ke a karamar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa a ranar Talata da ta gabata missalin karfe goma shadaya 11 na safiya.
Ko da shike har yanzu ba a iya gane sanadiyar kamun gobarar wutan ba, amma a bayanin Alhaji Sani Yusuf, babban sakataren hukumar SEMA ta Jihar, ya bayyana da cewa “gobarar ya fara ne missalin karfe goma shadaya 11 ta ranar Talata, 19 ga watan Maris har zuwa da maraice missalin karfe shidda 6, kamin dada wutar ta lafa” inji shi.

“Ko da shike damuwar mu a yanzun nan ba ta zancen gidaje, hatsi ko dabbobi da suka mutu da konewa muke ba, amma batun yadda zamu iya taimaka wa mutanen a cikin wannan mawuyacin hali da suke chiki. Yadda zamu samar da abinci, kayan sawa da wajen kwanci” inji Sani.

“Bayan mun magance wannan, sai mu dawo ga zancen yadda abin ya faru”
Ya kara bayyana da cewa ba wanda ya mutu sakamakon gobarar wutan, amma anyi rashin gidaje, hatsi da kayakin zaman al’umma”

Mun ruwaito a baya a Naija New Hausa da cewa gobarar wuta ya kame wata gida da mutane 6 ke cikinta a Jihar Kano, ya kuma kone da su duka kurmus, ba wanda ya tsira.