Labaran Nishadi
Ummie tayi Hatsarin Mota, ta kuma Mutu a yayin zuwa bautar kasa (NYSC)
Naija News Hausa ta gano da rahoto wata Yarinya da ta mutu a yayin da take hanyar zuwa wajen hidimar bautan kasa (NYSC) a Jihar Kaduna.
Mun ruwaito a Naija News Hausa ‘yan lokatai da suka gabata da cewa wasu ‘yan hari da makami sun sace Matan wani Lauya a Jihar Nasarawa a lokacin da suke kan hanyar zuwa Keffi don hidimar bautar kasa (NYSC)
Rahoto ya bayar da cewa yarinyar da aka gane sunanta da Agomie Ummie Mimie ta mutu ne sakamakon wata hadarin mota.
Mun gane da wannan rahoton a gidan yada labaran mu a yayin da daya daga cikin abokiyar ‘yar maccen ta bayyana hakan a layin yanar gizon nishadi ta facebook nata a yau Alhamis, 28 ga watan Maris 2019.
Abokiyar da ke da likin sun Xflex, kamar yadda ta sanya a facebook nata, ta bayar da cewa abokiyarta ta mutu ne sakamakon hadarin mota a hanyar Kaduna ranar Laraba, 27 ga watan Maris da ya gabata.
Kalli Sakon a Kasa, kamar Yadda Abokiyar ta bayar a layin facebook;
Story of a very young beautiful sister who lost her life in a car accident yesterday on27/03/2019Agomie Ummie Mimie by…
Posted by Etz Matthew Xflex on Wednesday, March 27, 2019
Naija News Hausa ta gane da cewa Ummie ta gama karatun babban Makarantan Jami’ar ta ne a Makarantar Ahmadu Bello University Zaria, inda ta karanci Yadda Ake Yada Labarai, wanda aka fi sani da (Mass Communication)
Karanta wannan kuma: Sheikh Ahmad ya samu Tsira daga hannun ‘yan hari