Uncategorized
Hukumar Kwastam ta fito da fom na daukan Ma’aikata 3,200, Kalli yadda za ka cika a kasa
Hukumar Kwastam ta kasar Najeriya, NCS ta gabatar da fitar da Fom ga masu neman aiki ga hukumar a shekara
ta 2019.
Naija News Hausa ta gane da wannan sanarwan ne bisa wata gabatarwa da Umar Sanusi, Kwanturola Janar na
hukumar yayi ga manema labarai a birnin Abuja a ranar Talata da ta gabata.
Ya gabatar da cewa hukumar zata dauki ma’aikata kimanin mutane 3,200 a dukan jihohin kasar a shekara ta
2019.
Ya kuma ci gaba da bayyana yadda tsarin zai kasance, kamar haka;
– Za a dauki Mutane 800 a – Support Staff for Superintendent Cadre
– Za a kuma dauki Mutane 2,400 a – Custom Inspector da kuma Customs Assistant Cadre
Kana iya bin wannan layin www.vacancy.customs.gov.ng don samun cikakken bayani da kuma yadda za a cika fom
din hade da sharidun da ke ga cika fom din.
Karanta wannan kuma: Hukumar Shiga da Fitan kasar Najeriya (NIS) ta gabatar da watsi da zance cewa suna daukar ma’aikata a halin yanzu.