Uncategorized
Karanta bayanin shugaban Miyyeti Allah ta Jihar Bauchi game da kashe kashen da ake yi
Kungiyar Miyyeti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN) ta Jihar Bauchi sun yi kirar kula ga Jami’an tsaron kasar Najeriya.
Naija News Hausa ta gane da cewa kungiyar tayi kira ne da bukatar hukumomin tsaro da Gwamnatin kasar Najeriya da magance matsalar hare-hare da kashe-kashen wata rukunin ta’addanci da ake cewa ‘Yan Ba Beli.
Wannan gidan yada labaran tamu ta samu rahoton ne bisa bayanin da sakataren kungiyar MACBAN, Alhaji Sadiq Ahmed ya bayar a wajen zana’izar mutane biyu da aka kashe a Jihar Bauchi ranar Lahadi, 29 ga watan Afrilu da ta gabata.
A bayanin Mista Ahmed, ya bayyana da cewa a halin yanzu ‘yan ta’addan sun riga da kashe mutane goma daga cikin ‘yan kungiyar su. Ya kuma bayyana cewa idan har ba a dauki mataki ta musanman ba game da wannan, “lallai zasu ci gaba da kashe-kashe, kuma wannan zai zama abin takaici a Jihar a yayin da za a karu da mutuwar mutane a Jihar.” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Idan har sun ci gaba da hari da kashin mutane da ke kauyuka ba tare da an dakatar da su ba, lallai ba da jimawa ba, zasu fada ga birane da hari” inji Ahmed.
A fadin Alhaji Ahmed, ya bayar da cewa kashe-kashen na karuwa a koyaushe a Jihar Bauchi. Inji shi “Jin kadan da ta gabata an kashe mutane biyu kuma a yankin Toro, wasu biyu kuma a Ganjuwa bayan an sace wani kuma a shiyar kasuwan Durum, aka kuma kashe shi da baya, sa ‘anan kuma aka kara kashe wasu mutane biyu a karamar hukumar Ningi.
Ahmed ya gabatar da rokon sa ga Gwamnatin Najeriya, ya kuma bada tabbacin cewa kungiyar tasu zata hada kai da Gwamnati da hukumomin tsaro don yaki da ta’addanci a Jihar Bauchi don tabbatar da zaman lafiyar al’ummar Jihar gaba daya.
“Ba mu cikin wannan kira da aka yi ga mutanen yankin da daukan matakin da hannun su na yaki da ta’addanci, wannan ba zai jawo abin kwarai ba”
”An riga an kashe mana ‘yan kungiya da dama, amma ba zamu iya barsu da neman ramuwa ba.”
Mun sanar a baya a Naija News Hausa da cewa Daktoci daga kasar Turai sun shigo Najeriya don binciken lafiyar jikin Sheik El-Zakzaky, shugaban Kungiyar ‘Yan Shi’a.
Bisa rahoto, Naija News ta gane da cewa an shigo ne da Daktocin don diban lafiyar jikin Sheikh ne da Matar sa. Wannan kuma zai dauki tsawon kwanaki kadan, bisa yadda aka bayar a rahoton.