Uncategorized
Ji abin da ‘yan HISBAH suka yi alkawarin yi ga wanda ya ki yin Azumi
‘Yan Kungiyar HISBAH ta Jihar Kano sun yi alkawarin kama duk wani Musulmi wanda ya kauracewa yin azumin watan Ramadan.
Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan HISBAH din sun rantse ne da cewa zasu kama duk wanda suka gane da cin abinci musanman a gidan abinci ko kan hanya, da cewa Ramadan dole ne ga dukan Musulmai.
HISBAH sun ranste da yin hakan, ko da shike sun bayyana da cewa wadanda kawai basu da lafiyar jiki da kuma aka basu sharadin su yi ta cin abinci daga asibiti ne kawai ba zasu kame ba don rashin yin azumin.
“Zamu kame kowa da muka gane da cin abinci a wannan lokacin azumin, har ma da wadanda basu da lafiya, sai idan har mun samu tabbaci daga Daktan da ke kula da su da cewa ya zamana dole su ci abinci”
Kwamandan Kungiyar HISBAH na Jihar Kano, Nabahani Usman ya bayyana hakan ne ga manema labaran BBC a wata gabatarwa.
“Muna yin irin wannan bincike ne kowace shekara, kuma za mu ci gaba da hakan a wannan shekara. Manufar hakan kuwa ita ce don sa kowane Musulmi ya girmama watan Ramadan.”
“Ko da ace likita ya ce fada maka da cewa kada ka yi azumi, wannan ba yana nufin kawai bane ka ci abinci a fili yayin da wasu suna azumi. Saboda haka duk wani musulmi da muka gane da cin abinci a waje, darukan mu za su kama shi kuma su kawo mutumin a ofishin mu, har sai dai idan ya nuna hujjar cewa likita ya ce masa kada yayi azumi, “in ji shi.
Naija News ta gane da cewa an kafa dokar Shari’a ne a Jihar Kano tun shekara ta 2001, a jagorancin tsohon Gwamnan Jihar, Rabiu Kwankwaso, wanda ya kafa da rattaba hannu ga kungiyar HISBAH.