Uncategorized
Ganduje: An kara Kujerar Sarauta Biyar (5) a Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ba da izinin amincewa da kudurin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka a kan rabar da kujerar martaba na Sarakai a Jihar.
Mun Fahimta a Naija News Hausa cewa wannan ya biyo ne bayan Gwamnan ya yi alwashin cewa zai bada hadin kai ga tafiyar da duk abinda Majalisar Wakilan Jihar suka gabatar da shi a gabansa.
A halin yanzu, Jihar Kano ta kasance da rukunin Kujerar Sarauta Biyar, suna kamar haka; Kano, Rano, Gaya, Karaye da Bichi. Wannan matakin ya rage yanki da wadiyar kujerar sarautan Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano.
Hakan ya faru ne bayan da Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Laraba da ta wuce, suka gabatar da dokar amince da gyaran Dokar kananan Hukumomi Jihar Kano.
Kwamitin sun amince da cewa samar da karin kujerar Sarauta a Jihar Kano zai taimaka wajen samar da ayuka, rage jayayya, da kuma rikice-rikicen tsakanin al’ummar Kano.
KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Hari da Makami sun Kashe wani Sarki a Jihar Sokoto