Labaran Nishadi
Boko Haram: Karanta Bayanin Gwamnan Gombe, Dankwambo game da Leah Sharibu
Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya aika sakon tausayi da kuma barka ga layin yanar gizon nishadin Twitter, ga Leah Sharibu, ‘yar makarantar Dapchi da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace shekarar da ta wuce.
Wannan sakon Dankwambo, sakon musanman ce ga Leah a yayin da ta cika shekaru 16 ga haifuwa a hannun ‘yan ta’adda.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a yau cewa Leah ta cika shekaru 16 a yau Talata, 14 ga watan Mayu 2019, haka kazalika ta cika tsawon kwana 446 kangin Boko Haram.
Ka tuna da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun sace Leah ne tare da wasu ‘yan makarantan sakandiri a Dapchi a ranar 19 ga watan Fabrairun ta shekarar 2019.
Ko da shike Gwamnatin Tarayya tayi kokarin ribato wasu daga cikin yaran daga hannun Boko Haram, amma ba a saki Leah Sharibu ba don ta ki amince da yin murabus da Addinin ta na Kirista.
A cikawar Leah shekara 16 a yau, Gwamna Dankwambo ya rattaba wa yarinyar da kuzari da halin mazantaka na fuskantar irin wannan mawuyacin hali.
“Na Taya ki murna da cika shekara 16 ga haifuwa Leah. Ba za a taba manta da ke ba” inji Dankwambo.
Kalli sakon a kasa a layin Twitter;
Happy 16th birthday to Leah Sharibu.
Never to be forgotten! You are in our thoughts and prayers. Many happy returns. #FreeLeahSharibu pic.twitter.com/g4eHyk6toa
— Governor Dankwambo (@HEDankwambo) May 14, 2019