Connect with us

Uncategorized

Ba wanda ya isa ya dakatar da Hidimar Rantsar da ni a Sokoto – Tambuwal

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto yayi barazanar cewa ba wanda ya isa ya dakatar da hidimar rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Sokoto a ranar 29 ga watan Mayu ta shekarar 2019.

Naija News Hausa ta fahimta cewa Tambuwal yayi wannan furcin ne don ya gane cewa akwai wasu a Jihar da ke kokarin kadamar da tashin hankali da tada tanzoma a Jihar.

Tambuwal ya furta hakan ne a wata gabatarwa da ya bayar daga bakin babban mai bada shawarwari gareshi, Alhaji Yusuf Dingyadi, da zargin cewa akwai wasu da ke yawatar da karya da jita-jita a Jihar ta rabar da hankalin mutane cewa Kotu na batun tsige shi daga kujerar jagorancin Jihar, don baiwa Jam’iyyar APC da maye gurbin sa.

“An rigaya an kamala hidimar zabe, kuma mun ci zabe, mun kuma yi kira garesu da hada hannu da mu don kadamar da ci gaba a Jihar Sokoto, amma sun kaurace wa hakan, sun kuma kai kara a Kotu, tau mai zai hana su jira shari’ar da Kotu za ta gabatar? inji Tambuwal”

“Bai yiwuwa ka kai kara a Kotu sa’anan ka shiga mutane da ruduwa da yawatar da zancen karya tun kotu bata gabatar da tasu hukunci ba”

Tambuwal ya kara da cewa lallai ta hanyar bin doka da ta dace ne kawai za a iya tsige shi a jagorancin Jihar.

Ya karshe da gargadin ‘yan adawan Jihar da jiran hukuncin Kotun Karan Zabe kamin dada su ci gaba da jita-jitan su a Jihar.

KARANTA WANNAN KUMA; Kannywood: Kotun Majistare ta bada Umarnin kame Hadiza Gabon