Uncategorized
‘Yan Sanda da Hukumar NDLEA sun kame Masu sayar da Mugayan Kwayoyi a Adamawa
Hukumar ‘Yan Sanda Jihar Adamawa sun kama mutane shida da ake zargi da sayar da mugayan kwayoyi a jihar.
Mista Adamu Madaki, Kwamishinan ‘Yan sandan jihar ya bayyana hakan a yayin da yake mikar da wayanda ake zargin ga hukumar Bincike da Yaki da Amfani da Mugan Kwayoyi (National Drug Law -NDLEA), a wata hidima da aka yi a ranar Litinin nan birnin Yola.
Ya kara da cewa yana a shirye don yaki da ‘yan ta’adda da masu amfani da mugayen kwayoyi.
Ya bayyana cewa haka kazalika suka kame kimanin mutane 300 a wata kangin ‘yan ta’adda da ake kira “Shila boys” da zargin amfani da mugayan kwayoyi, ayukan fyaden dole da fashi, a watan da ya gabata.
Kwamandan Hukumar NDLEA, Mista Yakubu Kibo ya rattaba wa Jami’an tsaro da hada kai da su wajen yaki da mugan kwayoyi a Jihar.
Kibo ya bayyana cewa hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a Jihar zai taimaka wajen yaki da ta’addanci da amfani da mugan kwayoyi a Jihar.