Labaran Najeriya
Yan PDP sun ce, Shugabannin Miyetti Allah ke da alhakin kashe-kashe a Jihar Benue
Jam’iyyar PDP a Jihar Benue sun bayyana bacin ran su game da matakin da gwamnatin tarayya ta ki ta yi a kan zargin da ake yi wa shugabannin miyetti da laifin kisan gillar da aka yi a jihar.
A wata sanarwa da sakataren yada labarai na jihar ya yi, watau mai suna Bemgba Iortyom, yan Jam’iyyar PDP sun ce wannan hali da rashin nuna kulawa ta Jam’iyyar APC ga halin ta’addacin nan ya nuna rashin cancanci ga zaben shekarar 2019.
“Gwamnatin da ta ƙi ƙaddamar da masu aikata laifuka da ta’addanci har ma yan ta’addan sun nuna a fili cewa su ne da alhakin mugan hari da farmaki da al’umman yankunan ke fuskanta a yanzu nan. Wannan irin hali da Miyetti Allah ke yi a tsawon shekaru, ya nuna cewa wannan gwamnati da kuma yan bada tallafi ga siyasar ta ba su da wani abin alhairi ga kasan. sabili da haka bai cancanta al’umma gaba daya ta amince da su ba a zaben 2019 da ke a gaba. in ji Shi.
Naija News ta ruwaito Mutane na ba za su iya zuwa Kirsimati a gida ba don Makiyaya inji Uche Okafor
Jam’iyyar ta ce aiki mafi girma ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC shine ya samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
“Duk da haka, wannan Jam’iyyar ta yi watsi da wannan, sun bar mutanen Jihar da rashin taimakawa ga mugayan hari da farmaki da Makiyayan nan ke kawo wa.
Karanta kuma: Shugaba Muhammadu Buhari a bukin tunawa da ranar haihuwan sa na shekara 76 a garin Abuja, ya roki yan Najeriya su gane, su kuma fahimci manufarsa, a ba shi karin lokatai kadan da nan, a kuma ci gaba da taya shi da gwamnatin sa da addu’a.