Uncategorized
Ku tafi makaranta, Roko da yawace yawace ba al’adar Musulunci bane – Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya gabatar da karatun kyauta a Jihar ga ‘yan Firamare da Sakandare.
Ganduje ya bayyana da tabbaci cewa gwamnatin sa zata tabbatar da cewa fiye da Malam Makarantan Firamare da Sakandiri dubu talatin (30,000) sun samu kwakwaran karatu da takardun da ya dace a jagorancin sa.
Gwamna Ganduje yayi barazanar cewa duk yaron da aka iske yana yawo ba tare da ya je makaranta ba za a kama shi hade da iyayen sa, a kuma gabatar da su a kotu don hukunci.
Naija News Hausa ta gane da wannan bayani da shirin Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ne bisa wata gabatarwa da yayi a Gidan gwamnatin Jihar Kano, inda ya gabatar da karatun kyauta ta dole ga dukan yaran makarantan firame da sakandiri a Jihar Kano.
Ganduje ya fada da cewa gwamnatin Jihar Kano ta riga ta hada kai da sarkin Kano, mai martaba sarki Muhammad Sanusi II akan mikar da zancen ga Majalisar Jihar Kano don su rattaba hanu ga kafa dokar.
“Duk wani Iyaye da aka gane da kaurace wa kai yaransu makaranta bayan da Majalisa ta amince da hakan za a kame su” inji shi.
“duk yaron da aka iske yana yawo ba tare da ya je makaranta ba za a kama shi hade da iyayen sa, a kuma gabatar da su a kotu don hukunci. Yawace-yawace da roko kan hanya ba al’adan musulunci bane. duk wanda aka gane da hakan za a kama shi” inji Ganduje.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun Koli ta Jihar Kano ta Tsige Sarakai Hudu da Ganduje ya Nada.