An Yanka ta Tashi! Kotun Koli ta Jihar Kano ta Tsige Sarakai Hudu da Ganduje ya Nada | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

An Yanka ta Tashi! Kotun Koli ta Jihar Kano ta Tsige Sarakai Hudu da Ganduje ya Nada

Published

Naija News Hausa, bisa wata rahoto da aka aika a yau Laraba, 15 ga watan Mayu, an bayyana da cewa Kotun Koli ta Kano ta sanar da tsige sabbin Sarakai Hudu da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada makon da ta gabata.

Mun ruwaito a shafin labarai ta yau da cewa Masu Nadin Sarauta a Jihar Kano sun gabatar da Lauyoyi 17 don Kalubalantar Ganduje da Kara Kujerar Sarauta Hudu a Jihar Kano.

Naija News Hausa ta fahimta bisa zargin da ake da Ganduje da cewa ya gabatar da karin kujerar sarauta hudu ne a Jihar Kano don cin mutuncin Mai Martaba, Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, da kuma rage masa Ikon shugabanci a Jihar Kano.

Ko da shike Ganduje a baya ya bayyana da cewa “duk wani mai abun fadi ya ci gaba da yada yawun sa, mu dai ci gaba muke so zuwa Next Level a Jihar Kano” inji Gwamna Ganduje.

An bayyana da cewa Kotun Koli ta bayar ne da umarnin Tsige Sabbin Sarakan da Ganduje ya nada ne tun ranar Jumma’a da ta gabata, amma Ganduje yaki bin hakan, da fadin cewa umarnin ya iso ne bayan da ya riga ya gabatar da kuma mika sandar Ikon Sarauta ga sabbin Sarakan.

KARANTA WANNAN KUMA; Ba ni aka wa Duka ba, Bata mani suna kawai ake kokarin yi – Inji Shahararrar ‘yan Shirin Fim a Kannywood, Bilkisi Shema

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.