Uncategorized
Karanta dalilin da yasa Manyan a Jam’iyyar PDP zasu gana a yau
Kwamitin Gudanarwa na kasa (NEC) ta Jam’iyyar PDP zasu yi zaman tattaunawa a yau Alhamis, 20 ga watan Alhamis, 2019.
A fahimtar Naija News, Jam’iyyar Dimokradiyyar zata yi zaman ganawar ne don tattaunawa akan zaben gidan Majalisar Dattijai da aka kamala a baya.
Ka tuna da cewa wasu ‘yan mamban gidan Majalisar Dattijai a karkashin Jam’iyyar dimokradiyya sun kauracewa yarjejeniyar jam’iyyar akan zaben Ali Ndume a matsayin shugaban gidan Majalisar Dattijai tare da Umar Bago a matsayin kakakin yada yawun Majalisar Wakilai.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa dan takaran kujerar shugaban Majalisar Dattijai a Jam’iyyar APC, Ahmed Lawal ya lashe zaben shugabancin Gidan Majalisa na 9.
Haka kazalika Omo-Agege, ya lashe zaben Mataimakin Shugaban Majalisar.
Manyan daga Jam’iyyar PDP sun gane bisa sakamakon zaben gidan majalisar da cewa wasu mambobin daga Jam’iyyar PDP sun jefa wa dan takaran Majalisar daga Jam’iyyar APC kuri’ar su.
KARANTA WANNAN KUMA; Rektan Makarantar Fasaha ta Yola, Farfesa Abubakar Umar yayi bayani game da zancen iske Makamai a cikin Masallacin da ke makarantar.