Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 8 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 8 ga Watan Yuli, 2019

1. A Karshe Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga amince da AfCFTA

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna amincewa da hukumar African Continental Free Trade Area (AfCFTA), ta rattaba hannu ga takardan amincewa.

Wannan matakin ya sanya Najeriya a matsayi na 53 a tsarin kasashe da suka rattaba hanu da amincewa da dokar.

2. ‘Yan Sanda sun gabatar da shirin kame Sanata Elisha Abbo akan zargin da ake masa

Hukumar Jami’an tsaron Najeriya suna a shirye don kame Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa a gidan Majalisa, a karkashin Jam’iyyar PDP.

Naija News Hausa ta gane da cewa Hukumar tsaron tayi hakan ne akan laifin da Elisha ya aikata na dukar wata Mata makon da ta gabata a birnin Abuja, kamar yadda muka sanar a labarai makon da ta wuce.

3. Obaseki yayi bayani game da hargitsi tsakanin shi da Oshiomhole

Gwamnan Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki, ya bayyana yin watsi da jita-jitan cewa akwai hargitsi da rashin amincewa tsakanin shi da Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

A wata gabatarwa da Obaseki yayi a ranar Asabar da ta gabata a wata hidima a Jihar Edo, ya bayyana da cewa fadin wasu ne kawai da cewa akwai fada tsakanin sa da Oshiomhole.

4. Har yanzu Buhari yaki bayar da jerin sunan Ministoci ga Majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari, harwayau bai bayar da jerin sunayan Ministocin da zasu yi jagoranci da shugabancin sa na karo biyu, duk da cewa lokaci ya gabato ga Majalisa da yin kadamarwansu kamar yadda ta saba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Majalisar zata koma ga Akulkin su ne a ranar 26 ga watan Yuli ta gaba.

5. El-Rufai ya bayyana banbanci tsakanin Arewa da Kudun Najeriya

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana Arewacin kasar Najeriya da kasance a baya wajen ci gaba da a fanin Ilimi da kadamarwa.

El-Rufai a wata hidima da aka yi a Jihar Kaduna Asabar da ta gabata, ya gabatar da cewa Arewa ta kasance da yawar Matalauta a kasar Najeriya fiye da dukan yankunan kasar Najeriya.

6. Oshiomhole da Magu sunyi ganawar kulle don tsige ni – inji Okorocha

Kotun Kolin Tarayya da ke a birnin Abuja, ta bada umarni ga Hukumar kare Tattalin Arzikin Najeriya da yaki da Cin hanci da Rashawa (EFCC), da kuma Hukumar DSS da janye hidimar bincike da suke yi ga tsohon gwamnan Jihar Imo,  Rochas Okorocha.

Bayan hukunci Alkali Taiwo Taiwo a kotun Kolin, Okorocha ya bayyana a gaban kotun da cewa ya karbi sani daga wani jami’in hukumar EFCC da cewa Ciyaman na hukumar, Ibrahim Magu yayi wata ganawar kofa kulle da Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da neman yadda zasu tsige shi ko kuma sa a jefa shi a gidan jaru.

7. A karshe, Boss Mustapha yayi bayani game da sabin zabin shugaba Buhari

Boss Mustapha, ya bayyana murnan sa game da yada shugaba Muhammadu Buhari ya sake zaben sa a matsayin babban sakataren Gwamnatin Tarayya.

Magatakardan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi da ta wuce a birnin Adamawa, ko da shike ya fada da cewa Ofishin ya kasance da wuyan jagoranci.

8. Mun kan bincike ga zargin da ake ga Fatoyinbo – CAN

Hadadiyar Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) sun bayyana da cewa suna kan bincike game da zargin fyaden dole da ake ga shugaban Ikilisiyar Commonwealth of Zion Assembly da aka fi sani da (COZA), Pastor Biodun Fatoyinbo.

Naija News Hausa ta gane da cewa, Busola, shahararar mai daukan hotuna da kuma matar sananan mawaki a Najeriya, Timi Dakolo, ta zargi Faston Ikilisiyar COZA da yi mata fyaden dole shekaru 20 da suka gabata.

9. Hukumar Kwallon Kafa ta Egypt ta tsige Kocin ‘yan wasa bayan wasan su a ranar Asabar

An tsige Kocin da ke jagorancin kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Egypt, Mista Javier Aguirre, bayan da aka fid da su a tseren gasan kwallon kafa ta AFCON da ake a shekarar 2019.

Naija News ta gane da cewa hakan ya faru ne bayan da aka lashe ragar ‘yan wasan Egypt da gwal 1 a ganawar su da ‘yan wasan kwallon kafa ta South Afrika a ranar Asabar da ta wuce.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a Hausa.NaijaNews.Com