Connect with us

Uncategorized

Mutane 19 sun Mutu a Hadarin Mota a wata babban hanya a Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto a yau da wata hadarin Mota a Jihar Kano da ya tafi da kimanin rayukan mutane goma sha tara (19).

Bisa bayanin da Hukumar FRSC suka bayar a yau ga manema labarai, an bayyana da cewa hadarin ya faru da maraicen ranar Lahadi da ta gabata, a wata hanyar da motoci ke bi sosai a Jihar Kano.

“Hadarin motar ya faru ne a shiyar kauyan Dinyar Madiga, Kilomita 85 daga cikin birnin Kano, babban birnin Jihar Kano, da maraicen ranar Lahadi da ta wuce” inji Zubairu Mato, Ofisan Hukumar ‘yan Road Safety (FRSC).

“Akalla mutane 19 ne suka mutu a hadewar motoci hudu, da ya kunshi Bus biyu da wata kananan motoci biyu. Haka kazalika kusan mutane bakwai suka sami mumunar raunuka a hadarin” inji Mato.

Ofisan ya bayyana da cewa hadarin ya faru ne a yayin da motoci hudun ke kokarin kaucewa rami da ke a kan hanyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa mutane Shida sun mutu a wata Hadarin Mota da ya faru a kan babban hanyar Jihar Sokoto.