Connect with us

Uncategorized

Kalli Bidiyo: ‘Yan Shi’a sun Kashe jami’an tsaro biyu a zanga-zangar da suka yi a yau, a Abuja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mambobin kungiyar ‘Yan Shi’a da suka fita zanga-zanga a birnin Abuja a yau Talata, 9 ga watan Yuni, 2019 sun kashe ‘yan tsaro biyu da harbin bindiga.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa abin ya faru ne a gaban gidan Majalisar Dokoki da tsakar ranar Talata (yau), a lokacin da ‘yan kungiyar shi’a ke kokarin shiga kewayan gidan majalisar Dokokin kasar Najeriya da ke a Abuja, babban birnin Tarayya.

Da aka gane da hakan, sai aka yi gurguje da kulle kofar shiga gidan Majalisar.

Ka tuna da a wata rahoto da muka ruwaito a Naija News Hausa a baya, ‘yan kungiyar shi’a sunyi barazanar cewa idan gwamnatin tarayya ta ki sakin Elzakzaky, shugaban kungiyarsu da matarsa, da cewa zasu canza salon su ga gwamnatin kasar.

A wata bidiyo da aka bayar ga gidan labaran nan tamu a yau, ka ga yadda ‘yan kungiyar suka mamaye gaban gidan majalisar Dattijai da barazana da lallace motoci da kayaki a gaban Majalisar.

Wannan mumunar abin ya biyo ne bayan da Jagoran babban rukunin Majalisar Dattijai, Ado Doguwa, yayi alkawari ga kungiyar ‘yan Shi’a a lokacin da suka hari kofar gidan Majalisa da zanga-zanga a ranar Alhamis ta makon da ta gabata da cewa zai gabatar da bukatar su ga Majalisar Dattijai da sauran mamban Majalisar da hukumar tsaro don neman a saki shugaban Kungiyar su, Ibrahim El-Zakzaky da Matarsa.