Connect with us

Uncategorized

Kungiyar CAN tayi kira ga neman a kama Shugaban Miyetti Allah

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira da a tsige da kame Shugaban kungiyar Miyetti Allah a cikin gaggawa.

Naija News ta fahimci cewa ƙungiyar kiristocin kasar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da suka bayar a ranar Lahadi, 22 ga Satumba.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta yi kira da a kame shugaban kungiyar Miyetti Allah saboda bayanin sa na cewa ba za a sami zaman lafiya a kasar ba idan ba a kafa RUGA ba a duk yankin Najeriya.

CAN ta kara a cikin sanarwar da tada murya kan wata abin damuwa, watau ganawa da sabbin fuskoki a yankin kudu maso gabashin kasar.

Cibiyar a wata sanarwar da suka bayar a ranar Lahadin da ta gabata, wanda shugabanta a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar, Bishop Dr. Goddy Okafor da Sakatare, Dr. S.C Nwokolo, suka rattaba hannu, sun ce, ya kamata a kori irin wadannan sabin fuskoki don barin yankin.

Bayanin na kamar haka;

“Duk mutane da ba a san asalinsu ba, wadanda ke mamaye yankin nan, ya kamata jami’an shige da ficewar kasa da sauran hukumomin tsaro su dakatar da su.”

“Abin kaito” inji kungiyar CAN, ta fada da cewa “shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, Manyan Ma’aikata ga Shugaban kasa, (PGs) da mashawartan majalisa suna zaune ne a biranen, da barin mazauna a cikin kauye ba tare da damuwa da rayukansu ba.”

“Mun la’anci irin wannan dabi’a kuma mun umarce su da su koma ga kauyukan su, su fara aiki daga garuruwansu. Bari su dawo su zama masu tsaron ƙofofi a ƙauyukansu.”

Ya karshe da cewa;

“yakamata a rusa da yin watsi da zancen kafa RUGA. Don wannan, muna la’antar kalamai masu tayar da hankali da Shugaban Miyyeti Allah yayi, na bukatar neman RUGA a cikin dukkan jihohin kasar, har da cewa ba za a sami zaman lafiya a ƙasar ba idan ba a yi hakan ba.”