Uncategorized
An yi wa mutane shida rauni, wasu Fyaden dole a Jihar Delta
Wasu ‘Yan Hari da ake zargi da zaman Fulani Makiyaya sun yi wa kimanin mutane shida rauni a gonakin su a wannan karshen mako da ta gabata, a garin Uwheru a Jihar Delta.
Naija News ta sami bayani da cewa Maharan sun kuma yi wa fursunoni biyu fyaden dole a yayin da matan ke kokarin komawa gidajen su.
Daya daga cikin wadanan mutane da aka yi wa rauni ya ce “Dukanmu na cikin gonakin mu a lokacin da suka shigo da dabbobinsu. A yayin da muka yi kokarin tayar da murya, sun fado mana da hari suka guma gudu sun bar dabbobinsu”.
Naija News ta ruwaito Dan Majalisar mai wakiltar Ayamelum na Majalisar Dattijai na Jihar Anambra, Mr Uche Okafor, ya bayyana tayar da hankali na ayyukan makiyaya a yankin su.
Ya ce “Mutane na ba za su iya zuwa Kirsimati a gida ba don Makiyaya”
Wani kwamishinan ‘yan sandan Jihar Delta, Anthony Agbizi, ya tabbatar da harin kuma ya bayyana ga manema labaru a garin Asaba da ce wa an aika wasu ‘yan tsaro don neman Makiyayan.
Sarkin wannan yankin HRM, Agbavwe Afugbeya Oyise 11, ya yi kira da neman taimakon gaggawa da gwamnatin tarayya da kuma Gwamnan Jihar Delta, Dokta Ifeanyi Okowa, wajen dakatar da irin wannan harin.
“Wannan mugayen hare-haren ya yi yawa da gaske, kare lafiyar mutane na shi ne mani babban abu a wannan mawuyacin hali da muke cikin ta”. in ji Sarkin.
“Babu daman zuwa gonakinmu, Makiyayan suna yiwa matanmu fyade, abin tausayi ne, kuma abin kunya ce da kuma Haramtaccen abu a Yankin mu da kuma mulkina kuwa, musamman yiwa Matar gida ma fyade a garin Urhobo” in kira ga Jami’an tsaro da kuma Gwamnan Jihar Delta don taimakawa ga dakatar da wannan mumunar hali na Makiyaya.
Karanta kuma Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Shehu Shagari ya mutu