Labaran Najeriya
Hanyoyi 10 Da Buhari Ya ƙasƙantar da Osinbajo – Fani-Kyaode
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya wulakantar da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
Naija News ta bayar da rahoton cewa, wasu ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta kan yanar gizo sun yi wa Osinbajo ba’a akan yadda shugabancin kasar da kuma shugabansa Buhari ke wulakanta shi, musanman barin Abba Kyari da maye gurbinsa.
Wannan zargi da ba’ar ya biyo ne bayan da Abba Kyari ya tafi kasar Landan don mika wata dokar ta baci ga Buhari don ya rattaba hannu, a Landan ranar Litinin da ta gabata.
A diba da ganewar ‘yan Najeriya, sun bayyana da cea Osinbajo ne yakamata ace ya rattaba hannu ga dokar a yayin da shugaban ba nan.
Haka kazalika rahotanni suka kuma bayyana a ranar Laraba da ta wuce da cewa, Shugaba Buhari ya kori ma’aikacin mataimakansa 36 da ga ofishinsa.
Fani-Kayode a yayin da yake mayar da martani akan matakan a shafin Twitter nasa, ya lissafa hanyoyi guda 10 da aka kunyata da kuma ci mutuncin Osinabajo.
Hanyoyi 10 da aka ƙasƙantar da Osinbajo;
1. A lokacin da Jirgin sama ya fadi da Osinbajo, maimakon ya tafi asibiti don kulawa jikinsa, maigidan nasa ya bukace shi da ya ci gaba da raba kudin yan kasuwa (Trader Moni).
2. Ga shi a matsayin sa na SAN da Farfesa masani Shari’a, amma a ƙarƙashinsa ana yiwa dokar kasa saɓo: yana wakilcin wanda baida tabbacin karatun ilimin firamare ko ma ta sakandare.
3. An dauki Bil zuwa Burtaniya don maigidanka ya sanya hannu, aka kuma yada shi ga labarai don a bata maka rai.
4. A matsayin ka na Dan’Aike, maigidanka ya aiki karamin Minista ya wakilce shi a wani taron da kuka halarta tare.
5. Tabas a matsayin ka na dan aike na kwarai! Sun cire duk masu taimaka maka a aikci daga Aso Villa zuwa gidan haya a Maitama.
6. A matsayin ka na yaron aike, ka je da durƙusa a gaban Abba Kyari don dakatar da binciken ƙarar da ake yi a gareka.
7. Mun gaya muku wannan tun a farko da cewa hakan zai faru amma ka ƙi ji. A yau, shugabannin biyu, Tinubu da Buhari, da kake girmamawa suna adawa da kai.
8. Kayi hakuri! Da wannan wulakancin, An dauki takarda daga Najeriya zuwa Birtaniya zuwa ga mutumin da ba shi da lafiya don sanya hannu, ba tare da wata ma’amala a gare ka ba, wannan tabbaci ne da cewa kai cikakken yaro aike ne.
9. Abinda mamaki a yanzu shine, maigidanka ya kori wasu mataimaka da suke maka aiki guda 36 a ofishku. Shin kana jiran sai sun kulle ka da hana ka shiga Gidan Aguda kafin ka yi murabus da komawa gidanka a Ikenne?
10. Bamu damu ko tausaya maka da wadanan ba, kai ka so haka. A yayin da yake kasar Amurka yana shakatawa, ya tura ka zuwa garin Daura don halartar hidimar Turbaning na wani Babban Sarki da ba a san da shi ba. Abin takaici, Muna rokon Allah ya sa hankalin ka ya komo maka.