Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 12 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 12 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Kotun daukaka karar da ke Jagorancin Karar Gwamnan Oyo ta haifar da rikici

Kotun daukaka kara da ke garin Ibadan a ranar Litinin ya barke da rikici bayan da kotun ta yanke hukunci kan batun rikicin zabe tsakanin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Adebayo Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress.

Naija News Hausa ta tunar da cewa Kotun daukaka kara a jihar Oyo, a watan Mayu da ta gabata a wannan shekara ta yi watsi da takardar neman kara da Adebayo Adelabu, dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress ya nema na sake kirga kuri’un zaben ranar 9 ga Maris 2019.

2. Kotun Daukaka kara ta Yanke Hukuncin Karshe akan Abiodun da Akinlade

Kotun daukaka kara da ke a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta yi watsi da karar da Adekunle Akinlade ya yi a kan nasarar zaben Gwamna Dapo Abiodun a ranar Litinin.

Idan za a iya tunawa, Akinlade ya tsaya takarar gwamna a jihar Ogun a ranar 9 ga Maris a kan dandamali na Allied People’s Movement (APM) yayin da Abiodun ya hau kan karagar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

3. Balarabe yayi Magana kan Abinda Zai Faru Idan Nigeria Ta Rabu

Wani tsohon gwamnan jihar Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa, ya bayyana da cewa idan har Najeriya ta rabu, wannan ba zai kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta ba.

Ya lura da bayyana da cewa yankunonin kasar zata ci gaba da fama da irin wadannan matsalolin da ake kokarin tserewa.

4. Tsohon Ministan Man Fetur Tam David-West ya mutu

Dan shekara 83, Farfesa Tam David-West, babban mai goyon baya ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya Mutu.

Wannan gidan labarai na da sanin cewa Mista David West ya yi jagoranci a matsayin ministan man fetur da makamashi a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Muhammadu Buhari, da kuma yin Ministan ma’adanai, Wuta da Karfe a karkashin mulkin Janar Ibrahim Babangida, a shekarun da suka gabata.

5. CAN ta bada bayani Kan Rikicin da ke Tsakanin Osinbajo da Babbar Shugabarsa, Buhari

Adebayo Oladeji, kakakin yada yawun Samson Ayokunle, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ya lura cewa babu wani rikici tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasar, Yemi Osinbajo.

Duk da haka, ya bayyana da cewa kungiyar ba sa farin ciki ba game da rahotannin da suke karba game da Osinbajo a kwanakin nan.

6. SERAP Ta Roki Babban Bishop na Canterbury Saboda Ci gaba da tsare Sowore da aka yi

Kungiyar Hakkin dan adam da cigaban tattalin arziki, (SERAP) ta wallafa wasika ga Archbishop na Canterbury, Revd Justin Portal Welby game da ci gaba da tsare jagoran #RevolutionNowMovement Omoyele Sowore da ke a hannun hukumar DSS.

Naija News ta tuno da cewa an Tsare Sowore ne a kurkuku daga hannun hukumar DSS bisa tuhumar sa da wasu laifuna bakwai da ake masa na cin amanar kasa, zamba, furcin rikici a yanar gizo da kuma cin mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari.

7. Gwamna Dickson yayi Magana kan Rikici da Goodluck Jonathan

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, yayi magana game da rashin jituwa da ake batu tsakanin sa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Dickson a cikin martaninsa ya zargi ma’aikatan siyasa da yin kalaman batanci tare da bayyana kalamansa da wata nufi da Jonathan game da zabin dan takarar gwamna na PDP.

8. Indimi ya Mayar da Martani ga Reno Omokri Akan Wata Furci

Babban Mai Arziki, Indimi tare da sauran Masu Kudi daga Arewa sun la’anci Tsohon Ma’aikaci ga tsohon Shugaban kasa, Reno Omokri, akan yabon Femi Otedola saboda gudummawar da ya bayar ga Arewa Maso Gabas ta hanyar ma’aikatar diyarsa, DJ Cuppy’s foundation.

Masu kudin sun mayar da martani akan furcin da Reno yayi ta kafafen sada zumunta.

9. Sakatariyar SDP ya Kone a cikin Lokoja

Rahotanni da suka iso ga Naija News ya bayyana da cewa an kona sakatariyar Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar rahoton da wakilinmu ya tattara, mutane da ba a san ko su wanene ba amma da ake zargi da zaman ‘yan tada zama tsaye wajen hidimar siyasa, sun kutsa cikin sakatariyar jam’iyyar SDP da sanyin safiyar ranar Litinin, suka kuma kone ofishin kurmus.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa