Uncategorized
Kotu Ta Umurci Dukan Tsohin Gwamnoni da Su Mayar da Kudin Fensho Da suka Karba
Dole Ne Saraki, Yari da Sauran Tsohin Gwamnoni su Mayar Da Fensho da suka Karba a Baya – Kotu ta fada wa AGF
Babbar Kotun Tarayya da ke a Legas, a cikin hukuncin da ta yanke, ta umarci Gwamnatin Najeriya ta kwato dukkan kudaden fansho da duk tsoffin gwamnoni suka karba da a yanzu duk suna zaman Sanatoci da Ministocin Tarayyar Najeriya.
Haka kuma Kotun ta umarci babban alkalin tarayya da Ministan shari’a, Mista Abubakar Malami (SAN), da ya kalubalanci gaskiyar dokar fensho na jihohi da ke baiwa tsoffin gwamnoni da sauran tsoffin jami’an gwamnati damar karban irin wadannan kudaden.
Naija News Hausa ta fahimci cewa wannan zancen ya biyo ne bayan wata korafi da SERAP ta yi kan yawan kudaden da jihohi ke kashewa ga biyan fensho ga tsohin gwamnonin jiha.
Ga sakon kamar yadda SERAP ta aika a layin sadarwa ta Twitter a Turance;
The court has adjourned to 3 February 2020 for report of compliance with the judgment by the Federal government.
We won't rest until this judgment is fully enforced and ALL state governors follow the Zamfara state example by immediately abolishing pension laws in their states.
— SERAP (@SERAPNigeria) December 4, 2019