Connect with us

Uncategorized

Tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo Ya Ziyarci Gwamnan Kaduna El-Rufai (Karanta Dalili)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin Soja da kuma mulkin farar hula, Olusegun Obasanjo ya ziyar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Obasanjo ya bayyana gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi dacewa mutum ya hada kai da su ga aiki.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kaduna lokacin da ya kawo wata ziyarar sirri ga El-Rufai a gidan gwamnatin jihar.

Naija News Hausa ta tuno da cewa El-Rufai ya yi aiki a karkashin Obasanjo, da farko a matsayin Darakta Janar, Ofishin Kamfanoni (BPE) sannan daga baya ya zama Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).

Wannan kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta kuma kula da cewa gwamna Nasir El-Rufai, kan nuna girmamawa, ya bar kujerar sa ta gwamna ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda ya ziyarci Kaduna.

Kodashike, wannan ziyarar sirri da tsohon shugaban ya yi wa El-Rufai ya haifar da bayyana ra’ayoyi jita-jita a da yawa kan kafofin watsa labaru. A yayin da ‘yan Najeriya da dama na zargin cewa Obasanjo ya ziyarci El-Rufai ne don rufin asiri kan zancen kamfanin wutan Lantarke ta (Discos).

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Ma’aikatan Kamfanin Wutar Lantarki Sun Dakatar Da Yunkurin Yajin Aiki Da Aka Soma

Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) ta dakatar da yunkurin yajin aiki da suka fara, ‘yan sa’o’i bayan da fadin kasar ta fuskanci rashin wutan Lantarki bisa mataki da ma’aikatar wutan lantarki ta kasar suka dauka.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Ma’aikatan Wutar Lantarki sun dakatar da yajin aikin ne bayan wani taro da wakilan Gwamnatin Tarayya suka yi a daren Laraba.