Labaran Najeriya
DSS: Karanta Bayanin Sarkin Musulmi Kan Kin Sakin Sowore Da Gwamnatin Buhari Ke Yi
Mai Martaba Sultan Na Sakkwato, kuma Shugaban Majalisar koli kan harkokin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya gargadi shugabanni kan duk wani yunkurin rashin biyayya ga umarnin kotu.
Ya yi wannan gargadin ne ranar Alhamis a Abuja a yayin taron kungiyar ta karo na hudu na Majalisar Tsakanin Addinin Najeriya da taken, ‘Addini da hukumomin farar hula kan tattaunawa don gina kasa.’
Shugaban addini da na gargajiyar ya yi gargadin cewa rashin biyayya da umarnin kotu wata alama ce da mafarin rashin bin doka da kuma tayar da rikici.
Kodayake Mai Martaba Sa’ad bai ambaci sunan kowa ba ga zancen, amma ana zato da imanin cewa Sarkin na magana ne kan tsananci da kin sakin Omoyele Sowore daga makamar hukumar DSS.
Ya lura cewa rashin jituwa da duk wani umarni na kotu ya kamata ne a sasanta hakan ta hanyar gabatar da karar rashin amincewa amma ba yin watsi da irin wannan umarnin ba.
Sarkin ya ce, “Dole ne mu yi biyayya ga dokokin kasarmu a kai da kai. Bai kamata mu yi watsi da ka’idodin ba domin guje wa sakamakon da zai biyo bayan hakan. Idan kotu ta yanke hukunci a kan wani lamari, to ya kamata a bi umarnin.”
Ya kara da cewa yin watsi da umarnin kotu ta kowane bangare na shugabanni daidai ne da kafa abin da bai dace ba da kuma hadari a nan gaba.
“Idan an bayar da umarnin kotu kuma da gangan ka ki yin biyayya saboda kai gwamna ne ko shugaban kasa ko wani mutum mai tasiri, to kuwa ka kafa abin da ke da hatsari.”
“Babu wata al’umma da za ta ci nasara ta wurin rashin adalci; Dole ne ‘yan kasa su bi doka don mu sami ci gaba da ake so,” inji Mai Martaba Sarki Abubakar.