Connect with us

Uncategorized

Jam’iyyar PDP Sun Dakatar Da Wani Sakatare A Jihar Filato

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Jam’iyyar Adawar Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP), a jihar Filato ta dakatar da sakataren jam’iyyar, Hon Emma Tuang, saboda rashin jituwa.

Kwamitin zartarwa na jihar ne suka dakatar da Sakataren a jihar Filato.

Dakatar da Emma ya bayyana ne a wani sanarwa da dan takarar gwamna a jam’iyyar a jihar, Jeremiah Useni ya bayar a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron SEC da aka gudanar a sakatariyar PDP a Jos.

Useni ya kara da cewa an kafa wani kwamiti da zasu binciki badakalar sakataren jam’iyyar.

A cewar rahoton, Tuang ya kira taron SEC a ranar Litinin din nan inda aka cire mukaddashin shugaban jam’iyyar, Hon. Amos Gombi tare da maye gurbinsa da Hon. Chris Hassan.

Dan takarar gwamna na PDP din ya bayyana cewa kwamitin da Barr. Simon Jok ke jagoranta, wanda aka bayyana Aminu Jonathan a matsayin Sakatare tare da wasu mambobi biyu, an basu makwanni biyu don gabatar da rahoton su.

“A taron SEC da PDP suka yi ya kai ga dakatar da sakataren jam’iyyar na jiha, Hon. Emma Tuang. An kafa kwamitin da zai bincike shi kuma idan an gano shi da wata laifi lallai za a cire shi.”

“Ga duk wanda yake karban umarni, ko dama daga wurin wani babba ne da ya dogara a gareshi da shawara, to yaje ya fada masa cewa ya bashi shawara da bai dace ba da kuma gaya mashi da cewa an hukunta shi.”