Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Asabar, 28 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Asabar, 28 ga Watan Disamba, 2019

1. Boko Haram: Shugaba Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya

An yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yarda ‘yan ta’adda su raba kasar biyu ta hanyar addini.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu da kuma aka bayar ga manema labarai a yau.

2. Jirgin Sama Dauke Da Tarin Mutane 100 Ta Rushe

Wani jirgin sama dauke da mutane 100 a cikinta ta fadi a Kazakhstan, inda tayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane goma sha hudu, bisa fahimtar Naija News.

A cewar jami’ai, jirgin na Bek Air ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga tashar jirgin saman ta Almaty da safiyar ranar Juma’a.

3. Tsohon Mashawarcin Tsaron Kasa, Dasuki Ya Bayyana Shirinsa Na gaba Bayan Sakinsa Daga Shekaru 4 Kame

Wani tsohon mai ba da shawara a kan tsaro na kasa (NSA), Kanal Sambo Dasuki, wanda ya samu ‘yanci kwanan nan bayan tsare shi da aka yi na tsawon shekaru hudu a kurkuku, ya bayyana cewa ba zai ba da wata hira ga manema labarai ba.

Dasuki, wanda shi ne Yarima na Khalifancin Sakkwato, ya yi wannan wahayin ne a cikin wata ganawa da manema labaran DAILY POST ta hanyar wani abokinsa, a Daren ranar Alhamis, 26 ga Disamba.

4. Jonathan Ya Shawarci Shugaba Buhari Kan Matakin Da Zai Dauka Ga Maharansa

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari da ta kama tare da tsananta wa ‘yan bindigar da suka kai hari gidansa a Otuoke, Jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, tsohon shugaban bai sami rauni ba a harin wanda mutane da yawa ke zargin cewa ana son ne kashe shi.

5. Shugaba Buhari ya bayyana Ra’ayinsa a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Lawan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake ba da shawara ga dan Lawan, Ibrahim, a wajen bikin auren sa.

6. Ohanaeze Sun yi Magana kan Tsige Shugaban kasa Buhari

Kungiyar gamayyar al’adu na Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta ce furcin da kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi na cewa akwai wasu rukuni a fadar shugaban kasa dake tafiyar da lamarin kasar ya isa ma kawai a tsige shugaban.

A cewar Shehu, Rukunin mutane ne masu nasarori da yawa ne da kuma girmamawa a kasar.

7. Wani Mutum Ya Bugi Matarsa Har Ga Mutuwa Ranar Kirsimeti

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun ta kama wani mutum da aka sani da suna Mutiu Sonola, da laifin buge matarsa Zainab, har ga mutuwa a ranar Kirsimeti.

Kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau da kullum a shafin Naija News Hausa