Connect with us

Uncategorized

Sabuwar Hari a Kauyen Rann, a yankin Kala Balge ta Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram sun kai sabuwar hari da ya dauke rayukan mutane kusan goma a yankin Kala-Balge, nan Jihar Borno

Mun sami sabon rahoto da cewa ‘yan ta’addan sun kai wa kauyen Rann hari, a inda suka kashe kimanin mutum 10 har ma sun bar wasu da raunuka da kuma kone gidajen kauyukan.

An sami tabbacin wannan ne daka wajen wani jami’in tsaro da ya bukaci kada a ambaci sunan sa.

Ya ce, “‘Yan ta’addan sun fado wa kauyen cikin wata babbar mota da daren jiya, litini 14, ga watan Janairu, 2019 inda suka hari wajen tsayin jami’an tsaron da ke yankin bayan sun kashe kimanin mutane goma 10, suka kuwa haska wa gidaje wuta har ma sun bar wasu da raunuka” in ji shi.

“Ganawar bude wuta tsakanin rundunar sojoji da ‘yan ta’addan ya dauki awowi kadan”

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Gwamna Kashim Shettima ya bayyana amincewa da fatan cewar Jihar Borno za ta komar da daukakar ta, a wata taro da aka yi a babban gonar Kashu da ke Maiduguri, nan Jihar Borno inda wasu manyan shugabannan jami’an tsaro suka halarta.

“Yanayin ya kasance da mumunar gani; rayuka goma sun tafi, mutane da dama sun sami rauni, sun kone gidaje mutanen harma sun fada wa wajen zaman hukumar UN da ke a Jihar a daren jiya” in ji wani da ya tabbatar da hakan.

“Mun iya kokarin mu tare da hadin kan wasu masu taimakawa wajen ganin cewa an samar da kulawa ga wadanda suka sami rauni” inji shi.

 

Karanta kuma: Rundunar Sojojin Najeriya sunyi barazanar cin nasarar yaki da ‘yan Boko Harama a garin Baga da ke Jihar Borno