Connect with us

Uncategorized

Abdulfatah Ahmed, Gwamnan Jihar Kwara ya dakatar da yawon yakin neman zabe a Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan ganin irin fade-fade, da hare-haren da ke faruwa a Jihar Kwara musanman makon da ta wuce, Gwamnan ya daga yatsa da cewar ya dakatar da duk wani yawon fita yakin neman zabe a Jihar.

A’a “Ta’addanci, Muzuntawa, Cin amana ko wata halin Tashin hankali abu ne da ba za mu yarda da shi ba a wannan Jihar” in ji Gwamna Ahmed.

Ahmed ya ce, wannan matakin zai dakatar da wadannan mugun hari da kashe-kashe harma da barnan tattalin arzikin jama’ar Jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa ‘yan ta’adda sun kai farmaki a gidan gadon babban shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki makon da ta gabata. farmakin ya faru ne a wata anguwa da suna Agbaji, anan cikin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, inda gidan gadon babban sanatan yake.

“Na dakatar da yawon yakin neman zabe don hana tashin hankali da farmaki a wannan Jihar” ganin irin mugun farmaki da tashin hankali da ya abku a cikin garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, in ji Gwamna Ahmed.

Bai tsaya a anan ba, Ahmed ya kafa hukumomin tsaro don kulawa da wannan hare-haren da kuma don dakatar ko hana duk wata tashin hankali da zai taso a Jihar. “Sai kawai Jam’iyyar da ta dauki dama daga Ofishin Kwamanda ‘yan sandan jami’un tsaron Jihar ne kawai za a ba dama da aikata wannan yawon yakin neman zabe” in ji shi.

Mun sami sani da cewa, Attahiru-Madami ya yi ganawa da Manyan mallaman gargajiya da yankuna da cewa su umurci mutanen su, su kuma ja masu kunne da dakatar da wannan mugun halin ta’addancin don samar da zaman lafiya a Jihar, harma ga zaben tarayya da ke gaba. An yi wannan zaman ne a birnin Ilorin a ranar 14 ga watan Janairu.

 

Karanta kuma: An yi wa tsohon shahararen dan Wasan Kwallon kafa na Najeriya, Kanu Nwankwo sata da barna a gidan sa da ke birnin Legas.