Hukumar DSS Sun Yi Koƙarin Sake Kamun Sowore Da Bakare

Bayanai da ke isa ga Naija News a yau safiyar Juma’a ya nuna da cewa jami’an ma’aikatar tsaro ta DSS sun yi kokarin sake kama Omoyele Sowore da Olawale Bakare.

Ku tuna da cewa su biyun an sake su ne kan beli daga hannun ‘yan sanda asirin ranar alhamis da yamma bayan hukuncin karar da kotu ta yanka.

Bisa rahoton da kamfanin dilancin labarai ta Sahara Reporters ta bayar wadda wakilinmu ya gano da ita, ta ce jami’an DSS sun kutsa kai ne a harabar kotun da safiyar Juma’a yayin da suke kokarin sake kama su biyun.

A cewar rahoton, jami’an DSS sun hana alkalin kotun, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu zama a kujerarta, har da cin mutuncin wani dan jarida a cikin lamarin.

A yanzu haka dai takaddama tana gudana a cikin harabar kotun yayin da jami’an hukumar DSS suka ki barin Sowore da lauyoyinsa su fita da kotun.

#RevolutionNow: A Karshe Hukumar DSS Ta Saki Sowore

A Karshe dai, Ma’aikatar hukumar tsaron Jiha ta Kasa (DSS) ta saki Omoyele Sowore, dan jaridan Sahara Reporters, da kuma jagoran zanga-zangar neman juyin juya hali, wadda aka fi sani da #RevolutionNow.

Naija News ta rahoto cewa an saki Sowore ne a ranar alhamis da yamma bayan ya share tsawon kwanaki 124 a tsare.

Wannan rahoton ya bayyana ne a yanar gizo, daga sanarwan Sahara Reporters, wacce Sowore da kansa ya mallaka.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar DSS da ta saki jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, da Olawale Bakare a cikin awanni 24.

Mai shari’ar, Ijeoma Ojukwu, wadda ta ba da umarnin ta kuma bayar da tarar N100, 000 akan DSS kan jinkirin da hukumar tayi wajen sakin Sowore da Olawale Bakare.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 6 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 6 ga Watan Disamba, 2019

1. Kotun Ta Saka Orji Uzor Kalu Ga Shekaru 12 a Gidan Yari

An yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari a hukuncin babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Alhamis.

Sanatan da ke wakiltar mazabar Arewacin Abia an same shi ne da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume 39 da aka gabatar a kansa.

2. Kotu ta Ba da Umarnin Karshe Kan Neman Takarar na uku Ga Shugaba Buhari

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Charles Enya, wanda ya shigar da karar neman a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar neman wa’adi na uku a karagar mulki ya janye karar.

Jigo a jam’iyyar ta APC a cikin wata sanarwa ya ce ficewar karar ya biyo ne don bada damar ci gaba da wasu bincike.

3. Kotu Ta Ba DSS Awanni 24 Don Sakin Sowore, Bakare

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar DSS da ta saki jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, da Olawale Bakare a cikin awanni 24.

Naija News ta fahimci cewa Mai shari’ar, Ijeoma Ojukwu, wadda ta ba da umarnin ta kuma bayar da tarar N100, 000 akan DSS kan jinkirin da hukumar tayi wajen sakin Sowore da Olawale Bakare.

4. Majalisar dattijan Najeriya ta zartar da kasafin kudin 2020

A ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba, Majalisar Dattawan Tarayya ta zartar da kudurin dokar kudi ta shekarar 2020, wanda ya karu daga jimillar kudi tiriliyan N10.33tn zuwa N10.6tn, fiye da yadda aka gabatar a da.

Wannan ya biyo bayan la’akari da zartawar rahoto da kwamitin majalisar suka bayar game da cancantar kudirin.

5. Kotu Ta Umurci Hukumar DSS Da Ta Mayar Da El-Zakzaky Ga Cibiyar Horon Al’umma

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta ba da umarni ga hukumar DSS da ta dauki shugaban IMN, kungiyar ci gaban Musulunci da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa Zeenat daga tsarewar ma’aikatarta zuwa cibiyar gyara halin al’umma ta jihar Kaduna.

Alkalin kotun ya bayyana da cewa yin hakan na da kyau don inganta da samun saukin saduwa da shi.

6. Ci Gaba Da Tsare Sowore, Halin Ta’addanci Ne – Soyinka ya gaya wa Buhari

Babban Marubuci a Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ci gaba da tsare jagoran kungiyan zanga-zanga wacce aka fi sani da #RevolutionNow, Omoyele Sowore, wani halin cin zarafi da ta’addanci ne.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta umarci hukumar DSS ta saki Sowore da Olawale Bakare a tsakanin awanni 24.

7. Majalisar Wakilai Ta Tarayya Ta Zartar Da Kasafin Kudi Ta 2020

A yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, Majalisar Wakilai ta Tarayya ta zartar da kudurin dokar kudi ta shekarar 2020, wanda ya karu daga jimillar kudi tiriliyan N10.33tn zuwa N10.6tn, fiye da yadda aka gabatar a da.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar ta gabatar da sabon adadi a yayin da ta gabatar da rahotonta game da kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Laraba da ta wuce.

Wannan ya biyo bayan la’akari da zartawar rahoto da kwamitin majalisar suka bayar game da cancantar kudirin.

8. 2023: Hanya Daya Kacal Da Kudu Maso Gabashin Kasar Zata Iya Lashe Kujerar Shugaban Kasa – Okorocha

Sanata da ke wakilcin yankin kudu maso gabas ta Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha ya ce yankin kudu maso gabas zata iya samun kujerar shugabancin kasar Najeriya ne a 2023 idan suka hada hannu da arewa da sauran bangarorin siyasar kasar.

Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba da ta wuce.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa

Kungiyoyi Sun Mamaye Birnin Tarayya Da Zanga-Zanga a Yau (karanta dalili)

A yau Laraba, 27 ga watan Nuwamba, Kungiyoyin fararen hula a halin yanzu suna mamaye birnin tarayyyar Najeriya, Abuja, don nuna rashin amincewarsu da yunkurin gabatar da Dokar Kalaman Kiyayya, wadda a turance aka kira ‘Social Media Bills’, da kuma nuna bacin ransu da ci gaba da tsare wanda ya gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore da gwamnatin kasar ta yi.

Naija News ta fahimci cewa Masu zanga-zangar sun tari kofar shiga majalisar dokokin kasar ne a Abuja.

Ka tuna Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a wata sanarwa da Naija News Hausa ta bayar makoni biyu da suka gabata, tayi Allah wadai da kudirin da majalisar dokoki ke gabatarwa na kudurin kisa ta hanyar rataye ga masu yada kalaman kiyayya, wadda Sanata Sabi Abdullahi ya gabatar.

PDP sun lura a cikin nuna rashin amincewarsu da cewa idan har aka tabbatar da wannan dokar kisa ga masu kalaman kiyayyar, lallai dokar zai raunana tsarin mulki da dokokin kasar, zai lalata tsarin dimokiradiyya, da kuma dakile ‘yancin’ yan kasa da kuma haifar da mummunan son kai a Najeriya.

Haka kazalika Naija News ta ruwaito a baya da cewa Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya

Kungiyar a wata sanarwa ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da jami’an tsaro da kuma bangaren shari’a don tsananta wa ‘yan Najeriya.

Kalli Hotunan Masu Zanga-Zangar a Kasa;

Sowore: Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya

Kungiyar Amnesty International a wata sanarwa ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da jami’an tsaro da kuma bangaren shari’a don tsananta wa ‘yan Najeriya.

Kungiyar yaki da haƙƙin ɗan Adam din ta bayyana hakan yayin da ta la’anci ci gaba da tsare jagoran ƙungiyar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ta hannun ma’aikatar tsaro ta DSS.

Naija News ta ruwaito a Manyan Labaran Jaridun Najeriya a baya da cewa a Ma’aikatar hukumar tsaron kasa (DSS)  sun harba tiyagas da bindiga don tarwatsa masu zanga-zanga da suka afka wa ofishinta don neman sakin Omoyele Sowore.

Deji Adeyanju wanda ya jagoranci zanga-zangar tare da mabiyansa sun mamaye ofishin hukumar ne a Abuja domin neman a saki Sowore nan da nan.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa zanga-zangar tasu ya biyo ne sakamakon jinkirta da hukumar DSS ke yi ga sakin Sowore, bayan da kotun koli ta riga ta bayar da umarnin a sake shi tun kwanakin baya.

DSS: An Bamu Miliyan Daya Don Dakatar Da Zanga-zangar sakin Sowore – Deji

Naija News ta ruwaito a Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta ranar Laraba da cewa Ma’aikatar hukumar tsaron kasa (DSS)  sun harba tiyagas da bindiga don tarwatsa masu zanga-zanga da suka afka wa ofishinta don neman sakin Omoyele Sowore.

Masu zanga-zangar, a karkashin jagorancin Deji Adeyanju, sun mamaye ofishin hukumar ne a Abuja domin neman a saki Sowore nan da nan.

Wannan matakin kungiyar ya biyo ne bayan da Lauyan Yaki da Daman bil adama, Femi Falana ya bayyana da cewa Omoyele Sowore, marubucin labarai na kamfanin dilancin Sahara da kuma jagoran #RevolutionNow ya cinma sharudan da ake bukata don belin sa.

Ka tuna a baya da cewa kungiyar Ci gaban Musulunci a kasa (IMN) wadda aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun hari Gidan Majalisar Dokokin Kasar Najeriya a birnin Abuja da zanga-zangar neman a saki shugaban kungiyarsu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da aka kulle tun shekarun da suka gabata.

Naija News Hausa ta tuna da cewa zanga-zangar ya haifar da mumunar yanayi, a yayin da wani shugaban Jami’an Tsaro da wasu ‘yan Shi’a suka rasa rayukan su a lokacin.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 22 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 22 ga Watan Oktoba, 2019

1. #RevolutionNow: Kotu ta rage Kudin Belin Sowore zuwa Naira miliyan 50

Mai shari’a Ijeoma na Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta duba yanayin belin da ya shafi Omoyele Sowore da Hukumar DSS.

A yayin da take bayani a ranar Litinin, lokacin da mai gabatar da kara na zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, ke neman sassauci kan yanayin belin sa, Mai shari’a Ijeoma ta ce za a iya rage belin Sowore ne zuwa miliyan 50 kawai, shi kuma Bakare zuwa miliyan N20.

2. Ngige Ya Bayyana Lokacinda Biyan mafi karancin albashi Zai Samu Tasiri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce cikakken aiwatarwa da kuma biyan sabon mafi karancin albashi zai gudana ba da jinkirta ba.

Naija News ta fahimci cewa Ministan kwadago da aiki, Chris Ngige ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kwanan nan a birnin tarayya, Abuja.

3. Benue: Gwamna Ortom Ya Gargadi Buhari Kan Makiyaya daga kasar Waje

Gwamna Samuel Ortom, Gwamnan jihar Benue ya bukaci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ya nemi hanyoyin hana makiyayan kasashen waje shiga Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Malama Wanhena Cheku ziyara, wacce makiyaya zuwa yiwa raunana a kwanakin baya da ake bawa kulawa a Asibitin Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Apir a Makurdi.

4. Kotu ta Ba da hukunci akan Gidan Saraki da ke a Ikoyi

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Legas ta ba da umarnin amshe Mallaka biyu a Ikoyi wacce ke da liki da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Mai shari’a Mohammed Liman ya ba da wannan hukuncin ne biyo bayan wani kara da Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gabatar.

5. Wanda ake zargi da Kisa, David West, zai bayyana a gaban kotu

Za a gurfanar da Gracious David West, wanda ake zargi da kisan gilla, a gaban babbar kotun jihar Ribas.

Ka tuna cewa wasu mutane da dama a jihar sun tada murya da kai tsaye kan kashe-kashen mata da ake yi Otal.

6. An rantsar da Edward Onoja a Matsayin Mataimakin Gwamnan Kogi

Anyi hidimar rantsar da Cif Edward Onoja, a ranar Litinin, 21 ga Oktoba 2019 a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi.

Naija News ta ba da rahoton cewa ‘yan majalisar sun tantance sabon Mataimakin gwamnan wanda daga nan suka neme shi da maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mista Simon Achuba.

7. Bankin duniya ta amince da bada rancen dala biliyan uku ga Najeriya

Babban bankin duniya ta amince da bukatar dala biliyan 3 da Najeriya ta nema don fadada hanyoyin rarrabar da kayan wutar lantarki a kasar.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, da take magana bayan amincewar wannan rancen a yayin taron bankin duniya, ta ce za a rabar da rancen ne a kashi hudu na dala miliyan 750 kowanne daga shekara mai zuwa.

8. 2023: Yadda Tinubu zai Iya samun kuri’u 20m Daga Kudu maso Yamma – Ogunlewe

Wani tsohon Ministan ayyuka, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya ba da sanarwar cewa Asiwaju Bola Tinubu, zai iya samun yawar kuri’u miliyan 20 daga Kudu maso Yamma shi kadai idan har ya yanke shawara ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Ogunlewe a cikin karyewar alkalummansa ya ce, Tinubu na iya samun kuri’u miliyan 5 daga jihar Legas shi kadai idan ‘yan siyasa daga yankin sun sanya himma a hidimar.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa 

DSS na Bayar da damar Amfani da Wayar Tarho ga kwamandojin Boko Haram – Sowore

Omoyele Sowore, mai gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow da kuma jagoran Kanfanin Dilancin yada Labarai ta Sahara Reporters, ya bayyana cewa ba a ba shi izinin amfani da wayar tarho ba yayin da yake tsare da ma’aikatar Tsaron Gwamnatin Tarayya (DSS).

Dan takar kujerar shugaban kasar a zaben 2019, Sowore ya zargi jami’an DSS da barin kwamandojin Boko Haram da aka katange a Ofishin Hukumar don yin amfani da wayar salula don sadarwa.

Naija News Hausa ta sanar a shafin Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta yau da cewa Mai shari’a Ijeoma Ojuwku na babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, ta ba da umarnin a tsare Omoyele Sowore a hannun Ma’aikatar Tsaron Kasa ta (DSS), yayin da za a saurari karar neman belin nasa a ranar 3 ga Oktoba 2019.

Wanan na biyo wa ne bayan da Sowore ya ki amincewa da kuma kin neman afuwa game da tuhume-tuhume bakwai da ake masa na zamba, cin amanar kasa, satar kudi da kuma yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini 30 ga Watan Satumba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 30 ga Watan Satumba, 2019

1. Gwamnatin Shugaba Buhari Na Shirin Karar Alkalin da ya yanka Hukunci Sakin Sowore

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin kai karar Alkali, Mai shari’a Taiwo Taiwo ga Majalisar Shari’a ta kasa (NLC) don bayar da belin da ya yi ga Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow.

Naija News ta tuna da cewa Babban Kotun Tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a Taiwo ta bayar da Beli ga Sowore wanda ake tuhuma da laifin shirin tayar da tashin hankali a kasa.

2. ‘Yan sanda sun Tabbatar da Karban Yancin Mahaifiyar Samson Siasia

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa Madam Beauty Ogere, mahaifiyar Samson Siasia, tsohon kocin ‘yan wasan Super Eagles, ta samu yanci daga hannun ‘yan Garkuwa.

Don bada tabbacin hakan, a ranar Lahadi Mista Asinim Butswat, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Sufeto Janar na ‘yan sandan yankin, ya ce rundunar ‘yan sanda za ta fitar da sanarwa ta musanman game da hakan ba da jimawa ba.

3. Gwamna Wike ya Tsoratar da PDP, APC Akan rijiyoyin Mai

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Enzo Wike ya gargadi sauran jihohi da karban rijiyoyin mai da ba bisa ka’ida ba na jihar.

Ya yi wannan gargadin ne yayin da yake zantawa wajen hidimar kadamar da Hanyar Birabi Street, Elegbam-Rumueme a karamar hukumar Obio / Akpor ranar Juma’a.

4. Tunde Bakare Ya Bayar da Sabon Bayani game da Karbar Muki bayan Shugaba Buhari

Babban Fasto da Janar Overseer ta Ikilisiyar Latter Rain Assembly, a jihar Legas, Fasto Tunde Bakare, ya ce faifan bidiyon da ya mamaye layin yanar gizo inda ya yi barazanar zama shugaban kasa, ya yi hakan ne kawai don bayyana burin sa.

Naija News ta tuno da cewa malamin ya shelanta a cikin wata Bidiyo da cewa zai karbi mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da wa’adinsa ya kare a shekarar 2023.

5. ‘Yan Sanda Sun Mayar da Martani akan Harin Banki a Abia

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Abia ta bayyana wani shirin da wasu gungun ‘yan fashi da makami yi don kai hari kan cibiyoyin ajiyar Kudade a Aba, babban birnin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron jihar (PPRO), SP Geoffrey Ogbonna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da manema labarai ranar Lahadi, a madadin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ene Okon.

6. DSS sun Kama wani Dan Yaki da Yancin Bil’Adama, Chido Onumah

Hukumar Tsaron Jiha-da-Jiha (DSS) sun kame wani Dan Yaki da Yancin Bil’Adama a Najeriya, Chido Onumah.

Naija News ta fahimta da cewa an kama mai yada labarai Onumah ne, a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe yayin da yake dawowa daga Barcelona, ​​Spain, inda ya kamala karatun digiri ga Sadarwa.

7. Shugabancin kasa ta Mayar da Martani ga Rashin Kasancewar Aisha Buhari daga Aso Villa

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin da ke cewa matar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta fita daga kasar zuwa kasar waje saboda takaddama da ke afkuwa a fadar Shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Uwargidan Shugaban kasar ta fice daga kasar nan kusan watanni biyu a yanzu, a sanadiyar rikicin da ke afkuwa a Aso Rock.

8. #RevolutionNow: Gwamnatin Tarayya da sanar da ranar sake Kame Sowore

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta sanya ranar Litinin, 30 ga Satumba, don gurfanar da jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, a gaban babbar kotun tarayya, Abuja.

Naija News ta tuna da cewa Gwamnatin Tarayya ta shigar da kararrakin da suka shafi hada baki da cin amanar kasa da kuma karkatar da wasu kudade a kan mawallafin SaharaReporters.

9. Shugaba Buhari Ya Tsige Shugaban Kotun Daukaka Karar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da korar Siaka Isiah Idoko-Akoh, Shugaban Kotun Shari’a Kan Zubar Jari da Tsaye.

Naija News ta samu tabbacin rahoton ne a wata sanarwa da sakataren din-din din na ma’aikatar kudi ta tarayya, Dr. Mahmoud Isa-Dutse ya fitar.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya ta kullum a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 7 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 7 ga Watan Agusta, 2019

1. Buhari ya bayyana ranar Rantsar da sabbin Ministoci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, 2019, don rantsar da sabbin Ministoci.

Naija News ta fahimta da wannan sanarwan ne a wata sako da aka bayar a layin yanar gizo ta Twitter, a ranar Talata, 6 ga Agusta da ta wuce.

2. Hukumar DSS ta Nemi Umurnin Kotu don tsare Sowore a Tsawon kwanaki 90

Hukumar Bincike da Tsari ta Jiha da Jiha (DSS), ta nemi dama daga kotu don tsare Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar neman juyin mulki, a tsawon kwanaki 90.

Ka tuna da cewa Hukumar DSS ta kame dan takaran kujerar shugaban kasar ne a zaben 2019, tun ranar Asabar da ta gabata.

3. Akeredolu ya hana Ma’aikatansa da Bayanin a Fili

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya umarci ma’aikatan gwamnatin jihar da su daina mayar da martani ga zantutuka ko wata kalamai, ko sanarwa game da ‘batun da ya shafi rikicin filaye.’

Wannan biyo ne bayan da aka kafa kwamitin kwamitin da zai binciki wata rikicin da ta kan filaye tsakanin jama’ar Araromi Obu da Ikale (Ago Alaye).

4. Daliban Jami’a ta Abubakar Tafawa Balewa sun mutu a yankewar Gada

Bayan yankewar Gada Sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da ya afku a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, jihar Bauchi, an ce wasu daliban sun mutu.

Bisa rahoton da aka bayar, Naija News Hausa ta fahimta da cewa gadar ta yanke ne sakamakon yawar ruwan sama, wanda ya kai ga sanadiyar mutuwa da bacewar wasu dalibai a yayin da suke dawowa daga karatun daga ajin su zuwa masaukin su.”

5. Reno ya la’anci hukumar EFCC da rashin tsige Shugaba Buhari bisa sakamakon WAEC

Tsohon ma’akaci ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya kwatanta Shugaba Muhammadu Buhari da Yahoo Boys a yayin da yake mayar da martani game da jirga-jirgan takardar shaidar jarabawan WAEC ta Buhari.

Omokri ya la’anci Hukumar da kamun Yahoo Boys da ke amfani da bayanai na karya don cutar mutane, amma da barin shugaba Buhari duk da cewa ya gabatar da takardann karya don yaudarar ‘yan Najeriya.

6. Ku Saki Sowore Nan da nan – Shugaban PDP ya gayawa Buhari

Shugaban jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, Uche Secondus, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da umarnin sakin Omoyele Sowore nan da nan.

Naija News ta bayar da rahoton cewa, shugaban PDP ya yi wannan kiran ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa a arewacin Najeriya ranar Talata, a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya ga gwamna Ahmadu Fintiri akan rasuwar mahaifinsa, Umaru Badami.

7. Hukumar INEC ta Bayyana yawan Karar Kotu da take gudanarwa

Hukumar gudanar da hidimar Zaben kasar Najeriya (INEC) ta zargi jam’iyyun siyasar kasar saboda yawan korafin da kotu ta yi game da batun zaben 2019.

A cewar shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana da cewa sama da kara 1,600 aka kai hukumar su a Kotu dangane da babban zaben shekarar 2019.

8. Falana ya gargadi Gwamnatin Tarayyar akan cajin Sowore zuwa Kotu

Femi Falana, babban maishawarci da fatawa a Najeriya (SAN), ya kalubalanci Gwamnatin Tarayya game da gurfanar da tuhumar da ake wa Omoyele Sowore, da cewa wannan zai zan babban kuskure idan har ta yi hakan.

Ka tuna cewa jami’an Ma’aikatar DSS sun kama Sowore, shugaba da kuma jagorar kungiyar #RevolutionNow tun Asabar bayan an zarge shi da yin barazana ga zaman lafiyar kasa.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa