Connect with us

Labaran Najeriya

Ina tabbatas maku da cewa Atiku zai kayar da Buhari a zaben 2019 – Aliyu Babangida

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Atiku zai kayar da Buhari

Babangida Aliyu tsohon gwamnan Jihar Neja, ya tabbatar cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, zai kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2019.

A jawabin sa da ‘yan jarida a Kaduna, tsohon gwamnan ya ce: “Ku yi imani da ni, ba kawai a jiha na ba, na yi imanin cewa idan zaben ba ayi juya-juya ko wata halin daru ba, kuma ya kasance da gaskiya, idan babu wata matsala, idan ba a yi amfani da jami’an tsaro ba don aikata mugun hali, za kuwa ci nasara. “Atiku zai yi nasara da Buhari.”

Aliyu ya kara da cewa, kada rashin amincewar Shugaba Buhari ga sanya hannu kan dokar gyaran zaɓen ya kirkiro wata matsala a kasar. Ya kuma sake kira ga shugaban kasa ya sake yin la’akari da amincewa da sanya hannun.

Ya ce: “Majalisar ta dauki mataki da ya kamata idan har su na da hali yin haka”.

“Amma idan za ta haifar da wata matsala a wannan lokacin, za mu iya jira. Na fahimci cewa daga cikin dalilan da shugaban ya bayas shine cewa dokar zaben zata fara ne a zabe na gaba ba wannan ba.

“Ina dubin da bukatar mu yi hankali a karkashin jagoransa, don tabbatar da cewa ba jawo wata matsala ba ga zaben 2019.

 

Naija News ta ruwaito Wakilin wakilai na wakilcin Kazaure/Geisel/Yankwashi a Jihar Jigawa, Mohammed Kazaure, ya lura cewa babu wanda zai iya rinjayar ‘Tsohon’ watau Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekara ta 2019.