Uncategorized
Ka mikar da kanka a sauwake ga ‘Yan Sanda, Femi Falana ya gayawa Dino Melaye
A ranar jiya Alhamis 3 ga watan Janairu, Femi Falana SAN, ya shawarci Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Jihar Kogi da cewa ya dace ya mika kansa a sauwake ga Jami’an tsaron ba tare da jinkiri ba.
Duk da haka, Falana ya kuma gargadi ‘yan sanda su gudanar da kama Melaye a hanyar da ta dace da kuma bin doka.
Ya kara a cikin maganar sa cewa, “Kowani mutum na da dama ya yi ra’ayinsa a kasar kamar yadda ta ke a cikin dokan kasa, amma shugabanci ko Jiha na iya karya wannan daman idar han an gane a bincike da cewa mutum ya aikata laifi da ta dace a hukumta shi”.
Ko da shike a nemi umurnin kama sanatan kwanakin baya har an sanar ga shugaban sanatoci, Bukola Saraki amma bai nuna kulawa ba ko daukan wata mataki.
Naija News ta ruwaito da cewa ‘Yan Sandan Najeriya da ke kewaye a gidan Sanata Dino Melaye sun yi barazanar cewa ba za su bar gidan ba sai har sun kame Sanatan.
Sanatan Melaye kuwa ya kaurace, kuma yaki ya bayar da kansa don a kama shi ba, duk da cewa jami’an tsaro sun kewaye gidan sa tun ‘yan kwanaki shidda da ta gabata da nan, amma ya ki fito wa don a kama shi. an kuma sanar da cewa jami’an tsaro sun yanke hanyar samar da wutar lantarki da kuma ruwar bulsatse a gidan.
“Wannan matakin dai bai daidanta ba ga ‘yan sandan bisa ga doka”. in ji Falana.
Amma dai shawara na ga Melaye shine ya mika kansa a sauwake don a kama shi ba tare da wata jinkiri ba, in ji Femi Falana.
Karanta kuma: Jihar Katsina na cikin mugun mawuyacin hali, in ji Gwamna Masari.