Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Mohammed Suka Baba yayi murabus da Jam’iyyar PDP ya koma APC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Zabe ya kusanto, kowa sai tsinke wa yake daga Jam’iyyar sa zuwa wata.

Tau ga sabuwa: Tsohon Mataimakin Mai yada Sawun Gidan Majalisar Jihar Kwara, Hon. Mohammed Suka-Baba ya saki Jam’iyyar PDP ya koma wa Jam’iyyar APC.

Suka-Baba ya ce “A matsayina na Fulani, na koma wa Jam’iyyar APC saboda Jam’iyyar da mutane na ke so kenan, kuma shi suka goyawa baya” Mohammed ya yi murabus ne da wasu ‘yan Jam’iyyar PDP da ke yankin Kaiama a Jihar Kwara, duka suka komawa Jam’iyyar APC.

Rahoto ta bayar da cewa Suka-Baba ya haska wa katin sa na zama dan mamban PDP wuta bayan ya juyawa Jam’iyyar baya, ya kara da cewar komawan sa Jam’iyyar APC sakamakon bukatar magoya bayansa ne. “sun bukace ni da komawa Jam’iyyar APC, kuma na koma.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Sanata Gamawa Babayo, Mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP ta Arewa ya koma wa Jam’iyyar APC bayan wata zargi da Jam’iyyar PDP suka yi masa.

“APC Jam’iyya ce na cin gaban kasa, kuma duk mai son cigaba dole ne ya goyawa APC baya a Jihar Kwara harma a kasar Najeriya gaba daya” in ji fadin Suka-Baba.

“Ba na bi Jam’iyyar APC ba ne don jawo wata matsala ko kawo damuwa, kuma zan yi iya kokari na don in shawarci ‘yan uwa da suka rage a Jam’iyyar PDP don su koma wa Jam’iyyar APC don samun cin gaba a kasar” in ji shi.

 

Kalla kuma: Farmakin da ta tashi a Yawon Yakin neman zabe da aka yi a Legas