Labaran Najeriya
Gwamnatin Tarayya da yarda da naira dubu 27,000 a matsayin sabon kankanin albashin ma’aikata
Bayan tattaunawa da gwagwarmaya tsakanin Kungiyar Ma’aikatan Kasar Najeriya da Gwamnatin Tarayya hade da Gwmanonin Jiha akan karin sabon albashi mafi kananci ga ma’aikata, Gwamnatin tarayya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari tare da tsohin Manyan Shugabanan, an kai ga amincewa da biyar Naira dubu 27,000 a matsayin albashi mafi kankanta ga ma’aikata.
Tattaunawar da aka yi a yau Talata, 22 ga watan Janairu, 2019 ta halarci Manyan shugabannai kamar tsohon shugaba Goodluck Jonatha, Abdulsalami Abubakar, Olusegun Obasanjo, Sanata Bukola Saraki tare da wasu Gwamnonin Jihohin kasar.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ma ya halarci tattaunawar tare da sauran shugabannai da ba a ambata sunayen su ba anan.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa shugaba Buhari ya Sanya Bismarck Rewane a matsayin Shugaban Kwamitin kadamar da Sabon Albashin Ma’aikata kasa.
Duk da cewa a baya Gwmanonin Jihohi sun yi ganawa da shugaba Buhari akan wannan shirin, inda Gwamnonin Jiha suka bayana ra’ayin su da cewa ba za su iya kai ga biyar Naira dubu talatin 30,000 ga ma’aikata ba, da irin bukatu da ayuka da kowanen su ke dashi a Jihar sa. Sun ce “Ba za mu iya cin ma biyar naira dubu 30,000 ba ga ma’aikata sai dai in za’a rage yawar ma’aikata a jihohi” in ji Gwamnonin Jiha.
Ko da shike an sanar a wajen tattaunawar da manyan shugabanan suka yi a yau da cewa a amince ne da naira dubu 27,000 kawai ga ma’aikatan, mun sami rahoto da cewa Shugaba Kungiyar Ma’aikata, Chris Ngige ya yi barazanar cewa dole ne Gwamnatin tarayya su karasa naira dubu 3,000 da ya ragu daga naira dubu 30,000 da kungiyar su ta bukaci gwamnatin tarayya su biya tun da farko.
An sanar da cewa za a mika wannan rahoto na sabon albashi bisa abin da gwamnatin tarayya da amince da shi ga gidan Majalisa a gobe Laraba, 23 ga watan Janairu don kara bincike da kuma amincewa.
Kalla: Bidiyon da ya nuna hotunan taron da Manyan suka yi a yau, inda Shugaba Buhari ya sha hannu da tsohon shugaba Obasanjo.
https://www.youtube.com/watch?v=9pCgIkOCGlw