Uncategorized
Ku bi dokar tuki, inji Alhaji Saidu bayan hadarin motoci biyu da ya dauke rai a Jihar Kano
Anyi wata muguwar hadari a Jihar Kano inda motoci biyu suka hade da juna harma mutum guda ya mutu, ya bar wasu kuwa da raunuka.
Hukumar Kashe Kamun Wuta na Jihar Kano sun gabatar da wata hadari da ya auku a hanyar Naibawa en’katako ta hanyar da ta bi Zaria a nan Jihar Kano.
Kakakin Hukumar, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayar da labarin hadarin ga Kungiyar Yada Labarai ta Najeriya, ya ce hadarin ya faru ne misalin karfe 8:50 na safiyar ranar Alhamis da ta gabata.
Yace, “Mun karbi wata kirar gaggawa ne ta wurin wani mai suna Ibrahim Mohammed daga nan yankin, ya kira mu na misalin karfe 08:52 na safiyar Alhamis da cewa motoci biyu sun yi hadari a shiyar harma wuta ya soma kame ko ina”.
“Jin hakan, sai muka kama hanya da motocin mu don kashe kamun wutar da kuma ribato rayukar da ke cikin motocin, mun kuwa isa ga wajen hadarin misalin karfe tara 9:00 na safiya, bayan mintoci kadan da hadarin ya faru” in ji shi.
Bayan isarmu a wajen, mun gane da cewa mota biyu ce da gaske, guda bas ce na daukar mutane, guda kuma babbar mota ce ta daukar kaya. “Motoci biyun sun yi gaba da gaba ne” in ji shi.
“Bayan bincike mun iya gane da cewa hadarin ya faru ne tsakanin motoci biyun sakamakon yawan gudu da mota ne tsakanin direbobi biyun” in ji Mohammed.
Ya ce, an rigaya an kai mutanen da ke cikin motocin zuwa asibitin Murtala Mohammed da ke a Jihar Kano don nuna masu kulawa ta gaske. “ko da shike bayan lokatai kadan mun sami bayyani daga bakin Dokta da ke kula da su cewa mutum guda ya mutu” sauran mutane bakwan 7 kuwa suna cikin tsanani, amma ana basu kulawa da ta dace.
Ku tuna da cewa mun sanar a Naija News Hausa kwanakin baya da cewa wata hadarin mota ya dauki rayuka uku da suka kone kurmus da wuta a sanadiyar wata hadarin mota da ta faru a wata Gidan man fetur nan yankin Okene, a Jihar Kogi.
Shugaban Hukumar Kashe Wutar ya shawarci direbobi da cewa su rika bin dokar tukin mota don dakatar da irin wannan mugun hadarin da ta dauke rai.