Connect with us

Labarai Hausa

Ku bi dokar tuki, inji Alhaji Saidu bayan hadarin motoci biyu da ya dauke rai a Jihar Kano

Published

on

Anyi wata muguwar hadari a Jihar Kano inda motoci biyu suka hade da juna harma mutum guda ya mutu, ya bar wasu kuwa da raunuka.

Hukumar Kashe Kamun Wuta na Jihar Kano sun gabatar da wata hadari da ya auku a hanyar Naibawa en’katako ta hanyar da ta bi Zaria a nan Jihar Kano.

Kakakin Hukumar, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayar da labarin hadarin ga Kungiyar Yada Labarai ta Najeriya, ya ce hadarin ya faru ne misalin karfe 8:50 na safiyar ranar Alhamis da ta gabata.

Yace, “Mun karbi wata kirar gaggawa ne ta wurin wani mai suna Ibrahim Mohammed daga nan yankin, ya kira mu na misalin karfe 08:52 na safiyar Alhamis da cewa motoci biyu sun yi hadari a shiyar harma wuta ya soma kame ko ina”.

“Jin hakan, sai muka kama hanya da motocin mu don kashe kamun wutar da kuma ribato rayukar da ke cikin motocin, mun kuwa isa ga wajen hadarin misalin karfe tara 9:00 na safiya, bayan mintoci kadan da hadarin ya faru” in ji shi.

Bayan isarmu a wajen, mun gane da cewa mota biyu ce da gaske, guda bas ce na daukar mutane, guda kuma babbar mota ce ta daukar kaya. “Motoci biyun sun yi gaba da gaba ne” in ji shi.

“Bayan bincike mun iya gane da cewa hadarin ya faru ne tsakanin motoci biyun sakamakon yawan gudu da mota ne tsakanin direbobi biyun” in ji Mohammed.

Ya ce, an rigaya an kai mutanen da ke cikin motocin zuwa asibitin Murtala Mohammed da ke a Jihar Kano don nuna masu kulawa ta gaske. “ko da shike bayan lokatai kadan mun sami bayyani daga bakin Dokta da ke kula da su cewa mutum guda ya mutu” sauran mutane bakwan 7 kuwa suna cikin tsanani, amma ana basu kulawa da ta dace.

Ku tuna da cewa mun sanar a Naija News Hausa kwanakin baya da cewa wata hadarin mota ya dauki rayuka uku da suka kone kurmus da wuta a sanadiyar wata hadarin mota da ta faru a wata Gidan man fetur nan yankin Okene, a Jihar Kogi.

Shugaban Hukumar Kashe Wutar ya shawarci direbobi da cewa su rika bin dokar tukin mota don dakatar da irin wannan mugun hadarin da ta dauke rai.

 

Karanta kuma: Ba mu amince da  naira dubu 27,000 a matsayin kankanin albashin ga Ma’aikatar kasa – inji hukumar ma’aikatan kasa (NLC) da kungiyar mallamai (NUT) 

Labarai Hausa

DSS Sun Kame Wanda Ya Shirya Bidiyon Shairi Kan Auren Shugaba Buhari Da Zainab, da Sadiya Farouq

Published

on

Ofishin Hukumar Tsaron Kasa (DSS) at sanar da kama Kabiru Mohammed, mutumin da ake zargi da kulla shellan karya kan auren Shugaba Buhari.

Naija News ta tuna cewa an bayyana wani rahoto a kusan  Oktoba ta shekarar 2019 cewa Shugaba Buhari ya shirya aure da Ministan Kulla da Al’umma, Sadiya Umar Farouq.

Day Dr. Peter Afunaya, kakakin yada yawun hukumar ke bada bayani kan lamarin, ya ce, an fara gudanar da bincike ne, biyo bayan korafin da Ministan Kudi ya yi wa Ma’aikatar.

Naija News ta fahimci cewa an kama Mutumin, mai shekaru 32 ga haifuwa ne saboda kirkirar wata bidiyo da kuma yada bidiyon karyar wanda ke nuna Shugaba Muhammadu Buhari na bikin auren Ministan Kasa, Zainab Ahmed da Ministan Harkokin Al’adu da Ci gaban Jama’a, Sadiya Farouq.

Ya bayyana da cewa sunyi kamun ne bayan da daga cikin Ministocin tayi gabatar da karar a ofishin su da neman su kame duk wanda suka gane da shirya da kuma watsar da bidiyon.

“Hukumar mu kuwa ta gane da kuma kame wanda ya shirya da kuma watsar da bidiyon. Sunansa Kabiru Mohammed. Dan Kano ne da kuma shekara ga 32 haifuwa. Ya kuma karanci yaran Fulfude da Hauda a makarantar jami’a ta Federal College of Education, Kano, da kuma karatun sashin Sadarwa daga Aminu Kano Islamic School.“

“Ya riga ya amince da aikata hakan kuma mun ci gaba da bincike kan dalilin hakan.” Inji shi.

Mutumin kuwa a ganewar Naija News Hausa ya nemi afuwa kan laifin sa da kuma bayyana cewa lallai aikin Sheidan ne. Ya kuma kara da cewa shi dan Jam’iyyar

Kwakwasiya ne a jihar Kano.

Continue Reading

Labarai Hausa

Gwamna Ganduje Ya Nada Mata Mataimaka na Musamman Guda 5 A Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya gabatar da nadin wasu mata Biyar a Kano

Wata tsohuwar Kwamishina mai kula da harkokin mata, Hajiya Hajiya Yardada Maikano Bichi, tana daga cikin mata biyar na Musamman Mataimaka, wadanda gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nada.

Gwamna Ganduje bayan nadin dukkansu da kuma bayar da umarnin su fara aiki nan take, ya umarci dukkan wadanda aka nada da su tabbatar da kwarewarsu yayin aiwatar da ayukansu a kowane ofishi.

A cewarsa, “tunda aka zabe ku a cikin jerin mutane da yawa, ya nuna a fili da cewa muna tabbatar wa jihar da cewa kuna da abin da zai kawo ci gaban jihar.”

“Ya kamata ku tabbatar da cewa kun bi dukkanin manufofin gwamnati da shirye-shiryen da suka danganci ofisoshinku, har ma da hakan, kuna kulawa da su da dukkan hankali.”

Wadanda aka nada sun hada da, Hajiya Fatima Abdullahi Dala, a matsayin mai ba da shawara ta musamman a shafin Kulawa ga Yara da kuma Ayukan Mata; Dokta Fauziyya Buba a matsayin mai ba da shawara ta musamman a Ma’aikatar Kiwon Lafiya; Hajiya Aishatu Jaafaru, mai ba da shawara ta musamman kan Shirin ciyar da ‘yan makaranta;  Hajiya Hama Ali Aware kuma a matsayin Mai Bada shawara na musamman akan Zuba Jarin Kasashen waje, da kuma Hajiya Yardada Maikano Bichi, a matsayin Mashawarci na Musamman kan Kungiyoyi masu zaman kansu.

Continue Reading

Labarai Hausa

‘Yan Hisbah Sun Kame Wani Dan Sanda Da Wasu Mata Uku a Gusau

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Zamfara ta bayyana kame wani jami’in ‘yan sanda da wasu mata uku da ake zarginsu da aikata muggan laifuka a wani otal da ke Gusau.

Shugaban hukumar, Dakta Atiku Zawuyya ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar hukumar ranar Litinin din nan da ta wuce.

Dakta Zawuyya ya bayyana da cewa an kama jami’in ‘yan sanda da ke aiki tare da ofishin‘ yan sanda ta Central Police Station da ke a Gusau tare da ’yan matan uku a wani ‘Otal, da zargin su da aikata laifin da suka saba wa ka’idar Sharia.

Zawuyya ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa daya daga cikin ‘yan matan uku da aka kama ta fito ne daga jihar Kaduna yayin da sauran biyun kuma ‘yan gida guda ne a Zamfara.

Shugaban ya ce hukumar sau da yawa ta gargadi masu kula da otal din kan amince da shigar da irin wadannan mutane a Otal din amma sun kasa bin ka’idoji da ke jagorantar gudanar da kasuwancin otal a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) sun bayar da rahoton cewa, jami’an hukumar Hisba sun kame harda Manaja da ke kula da Otal din.

Zawuyya ya karshe da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan cikakken bincike. (NAN).

Continue Reading

Trending