Uncategorized
Wata sabuwar Hari a Jihar Nasarawa, Gidaje 7 ya kone da wuta, mutum Ukku kuwa sun mutu
‘Yan Hari da bindiga sun kai wata sabuwa hari a Jihar Nasarawa
Kimanin mutane Ukku suka rasa rayukan su a Jihar Nasarawa sakamakon wata sabuwar hari da Mahara da bindiga suka kai wa Jihar.
Maharan sun fada Tudu Uku da ke yankin Toto a nan Jihar Nasarawa yau da safen nan inda suka kone gidaje har bakwai, suka kuma kashe mutane Ukku nan take.
“Abin takaici ne da irin yadda mahara ke kawo hari a wannan yankin har ma da kashe mutanen da basu aika wata laifi ba garesu, maharan sun kashe mutane ukku suka kuwa kone gidaje da kayaki masu tsadar gaske fiye da Miliyan da dama” in ji Mista Nuhu Dauda, Ciyaman na yakin Toto a nan Jihar Nasarawa.
“Ina mai kira ga masu aikata irin wannan mugun harin da su guje wa hakan, su tuba kuma su koma da zamantakewa ta lafiya da al’umma” inji shi.
“Na karbi sako ne game da harin da safiyar nan, da cewa ‘yan hari da bindiga sun kai hari ga Tudu Ukku harma sun kashe mutum ukku, sun kuma gunce wuyar wani, kone gidaje da babura, da kayakin mutanen da wuta da de sauran su, kuma na samu labari da cewa har yanzun nan akwai yaro da ba a gano ba” in ji Nuhu.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Wasu mazauna Jihar Nasarawa sun shaidawa Amnesty International (AI) da cewa ‘yan sanda da aka aika a yankin don magance matsalar makiyaya sun bukace su da biyar kudi mai kimanin naira Dubu dari da hamsin (N150,000) dan samar da tsaro a Jihar.
Ko da shike Shugaban Jami’an ya mayar da martani akan wannan zargin da cewa ba gaskiya bane.
Mista Nuhu Dauda ya bada tabbaci ga mutanen yankin da cewa yana a shirye don hada gwuiwa da jami’an tsaro a yankin don magance irin hare-haren da ake kaiwa yankin su.
Ka sami karin labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa