Labaran Najeriya
Islam: Kungiyar musulunci, JIBWIS zata gana da Buhari da kuma Atiku a birnin Abuja
shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wata taro na kungiyar musulummai da ake ce da ita ‘Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah, JIBWIS’ a birnin Abuja.
An sanar da cewa taron zai kasance ne a ranar Lahadi a birnin Abuja inda za a kadamar da wata bukatar kudi don sayan kayakin da zai taimaka ga samar da Ilimin Fasaha.
Mun samu wannan rahoton ne da aka bayar ta wurin sakataren kungiyar JIBWIS, Ahmad Muhammad Ashiru da cewa kungiyar zata gana da manyan ‘yan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC da PDP, da kuma Gwamnoni, Sanatoci, Gidan Majalisa Wakilai da kuma manyan ‘yan kasuwancin kasar tare da wasu ‘yan siyasa a kasar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wata kungiyar musulunci da aka fi sanin ta suna HISBA ta Jihar Kano sun kame Yan mata 11 dake shirin Auren Jintsi daya, watau macce da macce.