Connect with us

Uncategorized

Kimanin mutanen da Cutar Lassa Fever ta kashe a shekarar 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun sanar a Naija News Hausa a kwanakin baya da cewa cutar Lassa Fever ya kashe daya daga cikin Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a birnin Jos, Jihar Plateau.

Bayan wannan labarin, mun kara samun rahoto da cewa cutar ya sake kashe kimanin mutane biyar 5 a Jihar Plateau.

Ko da shike Dokta Chikwe Ihekweazu, yayi barazanar cewa Hukumar (NCDC) ta rigaya ta dauki matakai don dakatar da yaduwar cutar a kasar Najeriya.

A fadin sa, ya ce “Kada ku ji tsoro, muna shirin don dakatar da yaduwar cutar ‘Lassa Fever’, Wannan shine bayanin sa a birnin Abuja, makonnai da suka gabata.

A yau Litinin, 4 ga Watan Fabrairun, 2019, mun samu rahoto a Naija News da cewa cutar a shekaran ga da muke ciki ya kashe mutane kimamin 26 hade da wata cuta kuma da ake kira da ita ‘Meningitis’. An bayyana da cewa kimanin mutane 88 ke kame da wadanna cutar biyun a kasar Najeriya, musanman a Jihar Plateau.

Kamar yadda rahoto ta bayar a watan Janairu da ta gabata, kimanin mutane 77 aka samu da alamun cutar a Jihohin Najeriya goma sha ukku 13 har ma da birnin tarayya, Abuja tsakanin ranar 21 zuwa 22 ga Watan Janairu, 2019.

Ga takaitaccen kamuwar cutar ‘Lassa Fever’ da Cutar ‘Meningitis’ kamar yadda bincike ta bayar;

  1. Jihar Edo (24)
  2. Jihar Ondo (28)
  3. Jihar Ebonyi (5)
  4. Jihar Bauchi (3)
  5. Jihar Plateau (5)
  6. Jihar Taraba (3)
  7. Jihar Gombe (1)
  8. Jihar Kaduna (1)
  9. Jihar Kwara (1)
  10. Birnin Tarayya – Abuja (1)
  11. Jihar Benue (2)
  12. Jihar Rivers (1)
  13. Jihar Kogi (1) da kuma
  14. Jihar Enugu (1)

Binciken Hukumar NCDC ta kara bayyana da cewa mutane 11 suka mutu a Jihar Edo; Mutane 2 a Jihar Ondo; Mutun 1 a Jihar Benue, mutun 1 daga Jihar Rivers, Jihar Plateau da mutun 1, Taraba mutun 1 da kuma Jihar Bauchi da mutun 1.

Tsakanin 1 zuwa 27 ga Watan Janairu, mutane 538 aka iya ganowa da alamun kamuwar wannan cutar a shekarar 2019.

Kalla Bidiyon Cutar Lassa Fever: