Labaran Najeriya
Matan Shugaban kasa, Aisha Buhari ta dawo daga kulawa da lafiyar jikinta a Turai
Aisha Muhammadu Buhari, matan shugaban kasar Najeriya ta dawo daga kasan Turai inda ta je kulawa da lafiyar jikinta.
Mu na da sani a Naija News da cewa Aisha Buhari ba ta samu damar yawon hidimar yakin neman zabe da maigidan ta ba a watan Janairu da ta gabata, an bayyana da cewa matan shugaban ta yi tafiya zuwa Turai don kulawa da lafiyar jikin ta.
Ko da shike ba a bayyana ko menene sanadiyar rashin lafiyar Aisha Buhari ba, irin cuta ko illar jiki da ke damunta ba amma dai an gabatar da cewa ne kawai bata da lafiya kuma ta je Turai don kulawa da jikin na ta.
Duk da hakan mun samu rahoto a Naija News da cewa Aisha Buhari ta dawo daga kasar Turai, kuma ta yi ganawa da matan Jam’iyyar APC da Matasa a birnin Abuja daren Lahadi ta jiya.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Aisha Muhammadu Buhari ta bukaci Mata, da Matasa duka da su goyawa mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari baya ga zaben 2019 da ta gabato.
Ganawar da Aisha Buhari tayi a birnin Abuja da Matan Jam’iyyar APC tare da Matasa ya kumshi kimanin mutane 700. Matan shugaban ta kafa kungiyar ne don taimakawa mijinta wajen ganin cewa ya sake komawa ga kujerar mulkin kasar Najeriya bayan zaben watan Fabrairun da ta gabata.
Ga hotunan taron a kasa;
Karanta wannan kuma: Wani mutumi yayi wa matarsa duka wai don bata gaida kishiyarta ba