Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Mutane Hudu sun mutu a ralin shugaba Buhari a Jihar Rivers

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa kimamin mutane hudu ne suka rasa rayukar su a hidimar ralin neman zabe da Jam’iyyar APC suka yi a ranar Talata da ta gabata a birnin Plateau.

Hidimar da aka yi a babban filin kwallon kafa ta Adokiye Amiesimaka da ke a babban birnin Jihar Rivers, watau Port Harcourt, ya tafi da rayuka hudu. mutanen sun mutu ne sanadiyar yawar mutane da suka halarci hidimar don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya ga zaben 2019 da za a yi a ranar Asabar ta gaba.

An gano gawakin ne a bakin kofar shiga filin kwallon a yayin da mutanen ke gwagwarmaya da shiga filin don marabtan shugaba Buhari. “Mutanen sun fadi kasa don tsananin macewa, aka kuma tattake su har ga mutuwa”.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya aika wakilai a Jihar Taraba sun kai sakon ta’aziyya ga Iyalan mutanen da suka mutu sakamakon hidimar rali a Jihar.

An bada tabbaci da cewa an kai wadanda suka ji rauni a wajen ralin Jihar Rivers a Asibiti don nuna masu kulawata gaske.

Ganin irin yawar mutanen da ke mamaye hidimar ralin shugaba Muhammadu Buhari, ana iya mutun na iya bada gaskiya da cewa shugaban watakila ya sake cin zaben ranar Asabar.

Karanta wannan kuma: ‘Yan ta’adda sun Konne Ofishin Jam’iyyar PDP a Jihar Kano