Connect with us

Uncategorized

Hukumar NDLEA ta Jihar Gombe ta kame mutane 10 da ke sayar da miyagun kwayoyi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Kwamandan hukumar NDLEA na Jihar Gombe, Mista Aliyu Adobe ya gabatar da kame mutane goma (10) da ake zargin su da sayar da miyagun kwayoyi.

Hukumar ta kame su ne a yayin da ake zagaye da binciken lungu-da-lungu don tabbatar da tsaro da watsar da duk wata rukunin da zata iya jawo tashin hankali a lokacin zaben kasa da za a soma ranar Asabar ta gaba.

Mista Aliyu ya bayyana hakan ne ga kungiyar manema labaran kasar Najeriya (NAN) a ranar Talata da ta gabata a birnin Gombe.

“Mun kame su ne a shiyar Akko da Billiri ta Jihar Gombe da kuma karamar hukumar Kaltungo. Hudu daga cikin su na kara a kotu, sauran shiddan kuma, ana kan bincike akan su” inji Mista Aliyu.

“Zamu koma da zagayar yankunar nan  da muka kame su kamin ranar 23 ga watan Fabrairu da za a fara zabe” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa can baya da cewa Kwamitin Shugabanci da Manyan Sarakunan Arewacin Kasar Najeriya sun yi wata ganawa na tattaunawa akan anfani da Miyagun Kwayoyi da kuma Almajiranci

“Hukumar ta kuma gano wasu dake dilancin sayar da mugayen kwayoyin, zamu bi su kuma mu kama su”

“Za mu kuma kara zagaye da tabbatar da cewa ba a rabar da mugayan kwayoyin nan ba ga mashaya musanman a lokacin zabe” inji shi.

Ya karshe da bada shawara ga matasa, ya ce “Ku guje wa shan mugayan kwayoyin nan saboda illar su”