Uncategorized
PDP: Hukumar EFCC sun kame Lauyan Atiku
Hukumar Bincike ga Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) sun kame lauyan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Hukumar sun kame Mista Uyiekpen Giwa – Osagie ne da maraicen ranar Litini da ta gabata, akan wasu zargi 18 da ake tugumar shi da ita na cin hanci da rashawa.
Muna da sani a Naija News da cewa kwanakin baya an yi wa Mista Giwa-Osagie bincike aka wasu laifuka kamin nan.
Wata rukuni ta bayar da cewa wata kila mista Osagie da Jam’iyyar PDP na shirin yin amfani da kudaden ne da ake zargin sa da ita wajen gudanar da makirci da sayen zabe ga zaben shugaban kasa da za a yi a ranar Asabar ta gaba.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta bada zarafi ga Jam’iyoyi don ci gaba da kadamar da hidimar ralin neman zabe har zuwa ranar Alhamis na makon nan.
Ko da shike dai ba cikakken bayani akan kamun Mista Osagie a yanzun nan, amma ana jita-jitan cewa watakila kudin daman an boye su ne don sayan kuri’u daga jama.
Karanta wannan kuma: Ina ganin diyata a mafarki – inji Baban Leah Sharibu