Labaran Najeriya
2019: Shugaba Muhammadu Buhari da Matarsa sun jefa kuri’ar su
0:00 / 0:00
Tau, a karshe dai mun kai ga fara zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Mallaman zabe sun fara aikin su kamar yadda aka koyar da su, jama’ar Najeriya kuma sun fito makil don jefa kuri’a a matsayin ‘yan kasa masu fahimta da hikima.
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari shi ma da matarsa sun fito kuma sun jefa kuri’ar su, masoyin shugaban na ta kallo da kirari, ko da shike dai ba wanda ya ‘iya motsawa kamar yadda aka yi wajen rali, wata kila saboda hukumomin tsaro.
Da aka tambayi shugaban ko zai taya wanda ya lashe zaben murna, sai yace “e’ lallai zan taya kaina murna don na san cewa zan lashe zaben” inji fadin shugaba Muhammadu Buhari.
Kalli yadda ya jefa kuri’ar sa;
 
https://twitter.com/channelstv/status/1099205628839505921
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.