Labaran Najeriya
An mika wa Shugaba Buhari da Osinbajo takardan komawa ga shugabancin kasa
0:00 / 0:00
Mun ruwaito a bayan a Naija News Hausa da cewa hukumar INEC ta gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga lashe tseren takaran shugaban kasa ta shekarar 2019.
A yau Larabar, 27 ga watan Fabrairu, shekara ta 2019, daidai misalin karfe 2:40 na rana, bayan gwagwarmaya da jaye-jaye, da hidimomi don neman sake komawa ga kujerar mulkin shugaban kasa, an mika wa shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa ga mulki, Farfesa Yemi Osinbajo takardan sake komawa ga mulkin kasar Najeriya na wata tsawon shekaru hudu (4) kamar yadda dokan kasa ta bayar.
© 2024 Naija News, a division of Polance Media Inc.