Connect with us

Labaran Najeriya

Karanta bukatar Atiku ga Buhari a wata ganawar da yayi ranar Alhamis da Janar Abdulsalam

Published

on

A ranar jiya Alhamis, 28 ga watan Fabrairu, 2019, tsohon shugaban kasar Najeriya da kuma shugaban Kungiyar zamantakewar lafiyar kasar Najeriya, Janar Abdulsalam Abubakar ya jagorancin wata zaman tattaunawa tsakanin dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC da na Jam’iyyar PDP.

Naija News Hausa ta gane da cewa zaman ta halarci shugaban hukumar gudanar da zaben kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, dan takaran shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da mataimakinsa, Peter Obi hade da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo hade da wasu da ba a anbaci sunayan su ba a rahoton.

Bayan jayayya da maganganu a wajen tattaunawar, Atiku Abubakar ya bukaci shugabancin Muhammadu Buhari da wasu abubuwa guda biya (5)

Ga bukatun kamar haka;

1. A saki asusun ajiyar kudin ‘yan jam’iyyar PDP da aka dade.

2. Karkira zabanni da ke a gaba

3. Bincike da bin tsari ta farko kamin masu jefa kuri’a su yi zaben su a zabanni ta gaba

4. Hukumar INEC ta bayyana hidimar su ga ‘yan takara duka

5. Gwamnatin tarayya ta saki duk ‘yan siyasa da aka kame a hanyar da bata dace ba.

Atiku ya kara bayyana da cewa ba a taba zabe da ke da muni ba a kasar Najeriya tun lokacin da Najeriya ta fara dimokradiyya, kamar irin zaben ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

“Zaben ya kasance da mumunar makirci. An kuma yi watsi da ra’ayin al’umma” inji shi.

Janar Abdulsalami da mambobin kungiyar zamantakewan lafiyar kasa sun roki Alhaji Atiku Abubakar da kuma bukace shi da dakatar da duk wata shiri da zai jawo rashin zaman lafiya a kasar.

Karanta wannan kuma: Mahara sun kai wata sabuwar hari a yankin Jihar Zamfara