Connect with us

Uncategorized

An kashe wani akan gardaman wasan kwallon Barcelona da Real Madrid

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gardaman wasan kwallon kafa ya yi sanadiyar mutuwar wani a Jihar Kano

Wasan kwallon kafa da aka yi ranar Asabar da ta gabata tsakanin Real Madrid da Barcelona ya kawo jayayya tsakanin abokai biyu har an kashe mutum guda da kuma raunana wani.

Wasar da ta kare 1-0 tsakanin manyan Kulob guda biyun ya sa har gardama ta tashi tsakannin Abdullahi Haruna da abokin sa Mujitapha Musa. Gardaman ya tashi ne tsakanin Abdullahi da Mujitapha a yayin da wasar ta kare inda suka kafa baki ga hirar yadda wasar ta kasance.

Wannan mumunar abin ya faru ne a daidai misalin 11:21 ta maraicen ranar Asabar a shiyar Yakassai karamar hukumar Jihar Kano.

Mun gane a Naija News Hausa da cewa wasan kwallon kafa, musanman irin wannan kan jawo gardama amma bai a yi zaton cewa zai iya kai ga kashe dan uwa ba.

A bayanin kakakin yada labarai na Jami’an ‘yansandan Najeriya, DSP Abdullahi Haruna, ya gayawa manema labarai da cewa Abdullahi ya zaro yuka ne lokacin da gardamar ta yi karfi tsakanin shi da abokin sa. Rahoto ta kuma bayar da cewa Abdullahi ya kara yi wa wani mai suna Suleiman Muhammad rauni a wajen.

“Abdullahi ya soke dan uwar sa ne da yuka a gaban sa kamin dada ya karan yi wa wani rauni” inji DSP Haruna.

“An kai Musa zuwa asibitin Murtala Muhammad da ke a birnin Kano a gaggauce, amma abin takaici, Musa ya mutu kamin samun kulawa a asibiti” inji shi.

DSP Haruna ya kara da cewa hukumar tsaron ta riga ta kame wanda ya aikata laifin kuma zai a mika shi ga kotun kara don yanke hukunci a kansa.

Karanta wannan kuma: Rikici ta barke tsakanin ‘yan shirin Fim na Hausa